ZABEN FITAR DA DAN TAKARA MAFI TSADA A TARIHIN APC

0

ZABEN FITAR DA DAN TAKARA MAFI TSADA A TARIHIN APC

…..Fitar da Kansiloli da Ciyamomi
….. PDP ta samu kudin shiga
Abubakar Danmusa
@Katsina City News

An kammala zaben fitar da gwani a tsakanin wadanda za su yi wa jam’iyyar APC a takara a matakan Kananan Hukumomi na Ciyamomi da Kansiloli.

Wasu Kananan Hukumomin an fitar da ‘yan takarkarin ba tare da zuwa filin zabe ba.

Wasu kuma sai da aka je zabe aka bi layi sannan aka fitar.

A binciken da muka yi a duk inda aka yi zabe an kashe kudi na fitar hankali, wanda a tarihin zaben fitar da gwani na Kananan Hukumomi ba a taba yin kamar sa ba.

A wata Karamar Hukumar, wani ya boye wakilai masu jefa kuri’a har sai ranar zabe ya fito da su. An ce kowanne Wakili ya samu sama da Naira dubu 200. Sannan wasu ‘yan takarkarin ma sun ba su.

Wani Wakili ya tabbatar mana cewa ya samu dubu 320 cas!

A wata Karamar Hukumar kuma wani Dan Majalisar Tarayya ruwan dufana na kudi ya yi, tare da wasu alkawurra in har dan takararsa ya kai labari.

Wani Wakili ya ce; “Kudin da na kama ko a mafarki ban taba tsammanin zan mallake su ba a matsayina, amma sai ga shi ana ba ni, ana kuma cewa an gode.”

Wata Karamar Hukumar ita ma an ce akwai wani Dan Majalisar Tarayya ya yi wa masu zaben ruwan Nairori da alkawarin abin hawa. Dukkansu sun dara.

Irin wannan facakar kudi haka ta faru a duk fadin inda aka yi zaben na Kananan Hukumomi da wasu na Kansiloli.

APC ta yi zaben wadanda za su yi takara a kusan duk inda aka yi sasanci, cancanta da maslaha aka kalla a mafi yawan wuraren da aka yi haka an fitar da ‘yan takara da suka dace, kuma an yi maslaha ta aiki tare da ci gaba.

Amma mafi yawan inda aka yi zabe, kudi sun yi aiki. Akwai biyu zuwa uku da muka tabbatar da cancanta ta fi rinjaye.

A jam’ iyyar PDP kuma siyar da fom ga ‘yan takarkari ya samar masu da kudin shiga.

Wani jami’in jam’iyyar ya tabbatar wa da jaridun nan cewa, za a yi hidimar habbaka jam’iyyar ne da kudin da suka shigo.

“A karon farko tsawon lokaci, an zo taro duk mahalartansa sun samu lemun roba biyu da ruwa da rabin kaza, ” in ji mai ba mu labari.

@Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here