MATSALAR ZABEN DAN TAKARAR KARAMAR HUKUMAR SAFANA A APC

0

BIDIDDIGI;
MATSALAR ZABEN DAN TAKARAR KARAMAR HUKUMAR SAFANA A APC
@ Katsina city news
Jaridun katsina city sun kara bindiddigin zaben kabir Umar da akayi don ya yi ma jam iyyar APC takara a karamar hukumar safana.
Binciken mu ya tabbatar da lallai gwamnan katsina ya taba Sanya kwamishinan ilmi farfesa badamasi lawal ya binciki kabir Umar lokacin yana jami in ilmi na karamar hukumar safana.
Mun samu magana da wadanda aka Kira a matsayin shaidu a binciken. Mun samu tabbacin bayan da kwamishinan ilmi ya kammala binciken sa kafin ya rubuta rahoton shi.sai da ya Kira kabir Umar ya bashi damar kare kanshi. Bayan nan kwamishinan ya rubuta rahoton shi yaba gwamna.
Mun samu tabbacin a bisa wannan rahoton ne, gwamnan katsina ya Sanya aka rubuto ma kabir Umar takardar gargadi da Jan kunne.
Akan zargin yadda ake Sa banki nayi ma wasu masu aikin abincin makarantun ciyarwa ,kange kudin su .ko tsaida kudin kafin a biyasu.
Babban mai ba gwamnan katsina shawara akan wannan fanni.Alhaji abdulkadir mamman Nasir ya fada ma babban editanmu cewa, Sam su basu taba ba wani bankin umurnin ya rike kudin kowa ko ya rage ba.
Yace in har ana samun wani hadin banki tsakanin bankuna da jami oin ilmi wasu kananan hukumomi. wannan bada saninsu bane, kuma haram ne.
Binciken mu ya gano a tsakanin kananan hukumomi makwabtan safana .makarantun firamare na safana sune mafi koma baya. A wajen tsari da kuma cigaba.
Binciken mu ya gano in har ba jam iyyar APC wani gyara tayi ba akan takarar yankin.
Karamar hukumar safana na daga cikin wadanda jam’iyyar PDP na iya karbewa a zaben kananan hukumomi da za ayi a watan afrilu mai zuwa.
Domin jam iyyar PDP dinke take a karamar hukumar karkashin jagorancin Alhaji lawal Rufai safana. Ita kuma APC tana a cikin rudani.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777235

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here