Yadda Kwamitin Amaechi Ya Wanke Hadiza Bala Usman

0

Zargin Aikata Ba Daidai Ba:

Yadda Kwamitin Amaechi Ya Wanke Hadiza Bala Usman
Aliyu sale
@ katsina city news

Wani Kwamiti na mutum 11 da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya kafa don bincikar Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) da aka dakatar, Hadiza Bala Usman, ya wanke ta daga zargen-zargen da aka yi mata na aikata ba daidai ba da kuma facaka da kudaden Hukumar.

Hadiza Bala Usman, wacce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da ita biyo bayan zargin kin mika wasu kudade har Naira Biliyan 165 na rarar kudaden shigar Hukumar zuwa asusun Gwamnatin Tarayya, ta musanta duk tuhume-tuhumen da ake yi mata na aikata ba daidai ba.

Rahoton Kwamitin da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya da jaridar DAILY NIGERIAN ta yi tozali da shi, ya nuna cewa, ba a samu Hajiya Hadiza Bala Usman da aikata wani laifi a kan abin da ya shafi rashin mika Naira Biliyan 165 ga Asusun Gwamnatin Tarayya ba.

Kwamitin dai ya mika rahotonsa ne ranar 10 ga watan Janairu bayan ya kwashe watanni takwas yana zama, tare da zargin da ake yi masa na jan kafa a aikin nasa don ganin ya kawo cikas a kan umarnin Shugaban Kasa na dawo da Hadiza Bala Usman a kan kujerarta.

An dora wa Kwamitin alhakin gudanar da zuzzurfan bincike da nufin gano ko manufofi da kuma dabarun da Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya ta yi amfani da su, sun dace da tanade-tanade da dokokin Hukumar tun shekarar 2016 zuwa yanzu.

Wani bangare na umarnin da aika bai wa Kwamitin binciken ya yi nuni da cewa; “Ku bincika tare da duba dalilan da suka aka dakatar da wasu kwangiloli a Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, tare da tabbatar da cewa, ko wadannan matakan da aka dauka sun dace da sharru]a da kuma hukuncin kotu, tare da kuma bin umarnin da Shugaban Kasa ya bayar. Sannan a duba, tare da bincikar ko hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da lamarin sun dace da ka’ida da dokokin da ke gindaya wa Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya. A duba tare da bincikar ko sun yi daidai da dokokin aiwatar da kwangila na gwamnati da aka kafa tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu,”

Kodayake cikakken sakamakon binciken bai fito ba, amma wasu majiyoyi masu tushe da kuma bayanan da Jaridar DAILY NIJERIYA ta samu, sun tabbatar mata da cewa, Kwamitin ya gano Hadiza Bala Usman ta zuba Naira Biliyan 182.99 cikin Asusun Tattara Kudaden Shiga na Kasa da ake kira ‘CRF’.

“Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya ta ba da cikakken bayanai na yadda ta mika rarar kudaden da aka samu a Hukumar, wanda ake kira da ‘Operating Surplus Payments’ (CRF) ga Asusun Gwamnatin Tarayya, kuma ofishin Ma’ajin Gwamnatin Tarayya ya tabbatar da karbar kudaden.

“Bayani a kan matsayin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, duba da wasikar da ta fito daga Ofishin Tsara Kasafin Kudi na Gwamnatin Tarayya, sun bayyana ra’ayinsu karara na cewa: ‘…Aiwatar da kasafin kudi ba zai zama ma’auni na karshe ba na yanke hukuncin a kan yadda aka sarrafa rarar kudade ba. Saboda tsarin da aka tantance ne kawai hanyar da ake amfani da ita wajen tantance ku]a]en da aka kashe, kamar yadda yi a ko’ina a duniya, wanda kuma hakan ya dace da sashi na 22.2 da kuma na 23.3 na dokokin Tattalin Arzi}in Kasa (FRA) na shekarar 2007″.

Shi dai wannan sakamkon rahoton binciken, wanda ya mai da hankali a kan lokacin da Hadiza Bala Usman ta kwashe a kan kujerar shugabancin Hukumar, ya tabbatar da cewa, bayan nazari na tsanaki da bin diddigi da suka yi a kan bayanan da suka tattara, babu sabani tsakanin adadin kudaden da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya ta bayar da kuma bayanin da ya fito daga ofishin Akanta Janar na Tarayya.

“Aikin binciken da aka gudanar na hadin gwiwa tsakanin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya da ofishin Akanta Janar na Tarayya daga shekarar 2016 zuwa watan Mayu na 2021, sun nuna cewa an bi diddigin dukkan bayanan kudade da aka kashe yadda ya kamata, kamar yadda wasikar da ta fito daga ofishin Akanta Janar na Tarayya mai lamba R&I/021/B/367 ta ranar 30 ga watan Agusta 2021 ta nuna.

“Daga watan Janairu na shekarar 2016 zuwa Mayu, 2021, Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya ta zuba Naira Biliyan 182.99 a assusun Gwamnatin Tarayya. Kwamitin nan ya tabbatar da haka ne ta bayanan da suka fito daga Hukumar, tare da shaidun biya daga karamin ofishin Ma’aji na Gwamnatin Tarayya, sun tabbatar cewa, dukkan rarar kudaden sun shiga asusun Gwamnatin kamar yadda wasikar Akanta Janar na Gwamnatin Tarayya ta tabbatar mana”, kamar yadda wani bangare na rahoton ya nuna.

Duk da yake dai Kwamitin nan ya wanke Hadiza Bala Usman daga aikata ba daidai ba ko cin hanci da rashawa, amma duk da haka Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ba ta takardar gargadi, tare da zargin ta da ‘tsananin rashin ladabi’ a matsayinta na Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya daga ranar 18 ga watan Yuli 2016 zuwa ranar 6 ga watan Mayu, yana mai umartanta da ta amsa tuhumar a cikin kwanaki bakwai.

Wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ke kunshe a cikin takardar gargadin sun hada zargin rashin biyayya ga umarnin Minista, siyen manyan motocin da aka shirya amfani da su don shirin nan na ‘e-Call Up’, karya dokokin sadarwa tsakanin Hukumoin Gwamnati, siyen wasu motocin gudanar da ayyuka da sauran su.

A martanin da ta mayar mai shafuka 23, Hadiza Bala Usaman ta yi watsi da wadannan zarge-zargen da ake yi mata, tare da yin bayani dalla-dalla, inda ta tabbbatar cewa ba ta karya wata doka ba a matsayinta na Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya.

Da take tsokaci a kan zargin da aka yi mata na kin bin umarnin Minista, Hadiza Bala Usman ta bayyana cewa: “Hukumar Kula da Yadda ake Siyen Kaya na Gwamnati da ake kira BPP, ta mayar da martani ta wasikar da ta rubuto ranar 18 ga watan Yuni 2020 (an hada da kwafin wasikar a matsayin shaida ta 2) a shadara ta 6, BPP ta lura da bukatar karin wa’adin shekara daya da HMT ta nema ta kuma mika bukatar ga mahunkunta. A sakin layi na 7 na wasikar BPP ta nuna cewa, za ta amince da karin wa’adin wata 6 ne kawai, don Hukumar ta samu lokacin daidaita lamarin don ya yi daidai da yadda ake yi a kasashen duniya. An kuma sanar da wannan matsayar ga HMT ta hanyar wasikar da aka rubuta a ranar 30 ga watan Yuni 2020, wasika mai lamba MD/10/FMT/BOL.DD/366, an kuma hada da wasikar a matsayin shaida ta 2B.

“An wallafa takardar sanarwa ta soke lamarin a manyan jaridun Nijeriya biyu a ranar 8 ga watan Yuni 2020. Kuma an sanya a Mujallar ‘Federal Tenders Journal’. Wannan yana nuna cewa, ban taba kin bin umarnin Minista ba, kuma na isar da bukatar haka ne ga BPP. Amma Hukumar BPP ta ki amincewa da bukatar karin shekara daya, maimakon haka ma sai ta bayar da karin wata shida don Hukumar ta samu damar kammala shirye-shiryen da suka dace na ba da kwangilar. Duk wani musayar sakonni da aka yi da BPP a kan karin wa’adin wata shida an an yi shi ne don cika ka’idar doka, kamar yadda BPP ta umarta a wasikar da ta aiko a ranar 18 ga watan Yuni 2020.

“A kan zargin kin bin umarnin Mai Girma Minista na ranar 4 ga watan Mayu 2020 kuwa, ina so in sanar maka da cewa, musayar wasikar da aka yi da BPP ba an yi ne don a kara sabon wa’adin siyen wasu kayyaki ba ne, ko wasu bukatu da ke neman sai MTB ko FEC sun sani ba, amma wani lamari ne da ba sai an samu sanya bakin MTB da FEC ba. Don haka ba a karya wata doka ta HMT ta siyen kayayyakin aiki ga ma’aikata ba, ko kuma kin bin umarnin Minista ba, dole dukkan abubuwan da suka shafi saye da tallata ayyuka sun bi ta hannun Kwamitin Gudanarwa na Minista na ‘Ministerial Tenders Board (MTB)’, BPP, ko kuma FEC, kamar yadda yake kunshe a cikin wasikar da aka aiko ranar 4 ga watan Mayu 2020.

“Bisa wadannan dalilan na sama, ina mai tabbatar da cewa, ba a ki bin umarni, ko kin aiwatar da umarnin Mai Girma Minista ba ko kadan,” kamar yadda yake kunshe a cikin matartanin kare kai a kan zarge-zargen da Ministan Sufuri yi wa Hadiza Bala Usman.

A kan yadda aka sayi motoci biyo bayan barnar da zanga-zangar #EndSARS ya haifar, wanda ya kai ga lalata kayayyakin jama’a, ciki har da babbar hedikwatar NPA da ke Legas, Mista Amaechi ya tuhumi Hukumar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya a kan yadda suka sayi motoci na Naira Biliyan 1.277 don maye gurbin wadanda suka kone ba tare da amincewa Majalisar Zartarawa ta Kasa ba.

A martaninta, Hadiza Baka Usman ta ce: “A ranar Laraba 21 ga watan Oktoba 2021 zauna gari banza, sun kai hari Hedikwatar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya da ke Marina a Jihar Legas. Harin ya kai ga lalata babban ginin Hukumar da wasu gine-gine a wajen ajiye motoci da Cibiyar kashe gobara ta Ma’aikatar da dai saransu. Bayan barnar da suka yi wa gine-ginen, sun kuma kona motocin aiki da kuma dukkan motoncin ma’aikata da aka ajiye a warin adana motoci na ma’aikatan. Wasu motocin na daga cikin wadanda muke amfani da su na yau da kullum, muna kuma amfani da wasu wajen tattara kudaden shiga. Wannan barnar da aka yi wa Hukumar ta durkusar da Ma’aikatar, musamman abin da ya shafi tattara kudaden shiga da sauran gudanarwa. Don rage asarar da ake tafka, Hukumar ta dauki aniyar maye gurbin motocin ta hanyar tsarin gaggawa, wanda kuma ita ce hanya da fi dacewa da ya kamata mu bi a wannan lokacin.

“An bi ka’ida da doka wajen yin siyayyar ta hanyar bin ka’idojin da suka da cewa da sashi na 43 (1) (a), (2), (3) and (4) na dokar siyen kaya na Gwamnatin Tarayya na shekarar 2007 (PPA) kamar yadda muka kawo a kasa: 43-(1) “Za a iya yin siyayyen gaggawa kamar yadda wannan kudurin ya tanada;

“(a) Kasa na iya fuskantar wani tashin hankali ko bala’i ko kuma yaki, ko kuma wata jarabawa daga Allah.

“(2) In kana cikin wani yanayi na gaggawa, ana iya yin siyayyar kayayyaki ko samar da aiki kai-tsaye. (3). Duk siyayyar da aka yi karkashin lamari na gaggawa, za a dauke shi da muhimmanci, tare da kuma bin dukkan ka’idojin da suka kamata bisa lura da irin matsalar gaggawar da ake fuskanta. (4). Da zarar lamarin ya daidaita dole a samar da cikakken rahoto da za a mika wa BPP don sanya hannu, tare da ba da takardar shaidar “No Objection”. Ina mai jawo hankalinka a kan cewa, siyayyar gaggawar da aka yi ba ta saba wa sashi na 43-1, 2, 3 da 4 na dokokin PPA ba, kamar yadda muka kawo a sama. Ana ba Hukumar shawarar da ta gaggauta ci gaba da siyayyar da za ta yi ta gaggawa daga bisani kuma ta samar da cikakken rahoto da kuma takardar shaidar “No Objection”.

Jaridar DAILY NIGERIAN, ta fahimci cewa cikin tsohuwar Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, a zahiri ta warware zare da abawa a cikin amsar da ta rubuta mai shafi 23 a kan duk tuhume-tuhumen da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi mata.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here