AN GABATAR DA MALAM SHITU S SHITTU A GABAN KOTU

0

AN GABATAR DA MALAM SHITU S SHITTU A GABAN KOTU.
@ Katsina city news
A yau ne hukumar kwastam ta kasa ta gabatar da malam shitu s shittu gaban babbar kotun tarayya dake katsina.
Zama biyu kotu nayi, malam shittu bai samu halarta ba.
Amma a zaman yau duk wadanda ake zargi su uku sun halarta.
Alkalin ya shigo kotu da misalin karfe Goma na safe inda wadanda ake zargi suka shiga akurkin tuhuma.
Mai gabatar da kara ya karanta masu duk laifuffukan da ake Zargin su da aikatawa.
Wadanda duk suka musanta aikatawa.Masu gabatar da kara sun bayyana cewa suna da shaidu.
Inda aka daga Shari ar zuwa 5 ga watan April don cigaba da kawo shaidu.
Lauyan da ke baiwa su malam shitu, kariya ya Nemi a bayar dasu beli.
Alkalin ya amince.akan malam shittu ya kawo mutum daya mazaunin katsina da kuma bayar da fasgo dinshi na tafiye tafiye.
Akan bayar da fasgo ne, aka So a samu tsaiko inda da farko akace fasgo din yana Abuja.don haka suna neman a chanza masu wata kaidar ta beli.
Nan ne mai Shari a ya nuna cewa, in har babu fasgo ta a tafi da malam shitu gidan yari a ajiye shi daga baya a dawo kotu a Nemi sabuwar bukatar ta chanza kaidar ta beli.
Daga baya dai an kawo fasgo din.kuma an bayar dashi Belin da yamma sakat.
Shitu dai shine sakataren jam iyyar APC ta jahar katsina. Kuma makusanci ne ga daya daga cikin Wanda ake jin yana son tsayawa takarar gwamnan katsina.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here