WASAN WUTA A BIRNIN KIF (1)

0

WASAN WUTA A BIRNIN KIF (1)

Jiya ina tafowa gida ina sauraron wani Farfesa yana ta feso shirme akan rikicin nan na _Russia da Ukraine_ da yake su yawancin su su na debo abubuwan da kafafen watsa labaran Turai da ‘yan barandarsu suka sanar masu ne, amma a hakikanin gaskiya duk wanda bai san tarihin zamantakewa da fasalin wannan yanki na mutanen bakin ruwan Baltik ba, sannan kuma idan bai san akalla juye-juyen tarihin mutanen nan karnoni da dama ba bai kamata ya kama jagwalgwalo a radio ba.

Ina jinsa sama-sama hankalina na koma wa doguwar tafiyar da mukayi a jirgin kasa daga Birnin Moscow zuwa Stalingrad (tafiyar kusan awa goma a yammacin Russia, hannun riga da iyakarsu da kasar Yukreniya)

Yanki ne mai kyan gani kuma duk da tsananin sanyi (saboda zubowar dussar kankara kusan rubu’i ukku a shekara) amma duk da haka kana iya ganin itatuwa cikin furanninsu masu kyawu da dabbobi da tsuntsaye nata warkajaminsu a cikin daji)

Kila abokan tafiyata da dama a jirgin kasan basu san mugun tarihin da wannan hanya da ta dauko tun daga gabar tekun white sea zuwa Baltic ocean ta ratsa manyan garuruwan St Petersburg, Uryanovsk, Novgrod har ta shiga Birnin Moscow suka gani ba tsawon zamunna

Misali ta wannan hanya ne Mongolawa qarqashin Azzalumin sarkinsu Genghir khan suka shigo yankin na Baltic suka yi biji-biji da ilahirin Russia kacokaf din ta suka karmatse biranen Donesk har suka dangana da Birnin Qif (Kiev) din Ukraine, suna tafe suna fille kawunan maza da mata a ilahirin gabashin Turai bayan da suka gayawa mutanen Ubangiji ne ya aikosu su karkashe kowa saboda saba masa da suke yi, kuma abin mamaki Rashiyawa duk sun aminta tsananin sabonsu ga Ubangiji ne ya jawo masu kisa daga Wakilin Ubangijin (Sarki Genghis Khan). Wannan tun a qarni na 13 kenan.

Sannan ina iya tuna dai haka wannan yanki da muka bi a jirgin muka iske wata doguwar gadar sama kafin shiga Leningrad wacce ta shallake saman titin jirgin mu, a zuciyata ina cewa da wahala wannan ba gadar nan ta tarihi bace wacce ta ratsa ta nufi Birnin Kazan (a al’adata tun a Airport nakan siyi map duk kasar da muka je, amma saboda yanayin saukarmu Moscow tsakar dare ga yunwa sannan uwa uba kuma ba tafiyata bace ni kadai duk wadannan basu bani damar siyen taswirar kasar da har mafarke-mafarken ta nike ba kafin zuwa na saboda dimbin karance-karancen da nayi a kan su)

See also  BARAKA A TSAKANIN LADO DA MAJIGIRI

Idan har wannan gadar Kazan ce kuwa to zan iya cewa mun zo mahadar yakin daular Tzar karkashin Sarki Peter na 1 da Daular Usmaniyya ta Turkiyya (Ottoman Empire) karqashin Sultan Saleem na 2

Lallai an gwabza tsananin yaki kuma Rushiyawan sun samu nasarar danna tawagar musulmi har Constantinople, suka nutsatsa suka illata daular (kaman yanda Turawan Ingilishi suka yi biji-biji da Daular mu ta Sokoto) haka suka ratsa Caucasus suka kwace ilahirin lardin Budjek na Turkiyya suka shiga Azerbaijan suka kwace ikon Arewacin Iran suka danna mayakan daular har cikin Armenia.

Wannan yakin ne ya tarar da har rushewar Daular Ottoman a shekarar 1922 kafin Turawa ‘yan a yaga suka daka wawa ga ilahirin gabas ta tsakiya din!

Haka dai ta wannan hanyar ne dai a wannan yankin mayakan Nazin Hitler daga Jamus suka kuma kaca-kaca da Ilahirin gabashin Turai tun daga birnin Warsaw har sai da suka dangana da gaba dayan St Petersburg suna shinshino Moscow kafin Rushiyawan su tashi haikan su kwaci kansu, su korasu har Berlin su kwace Jamus din a abin da aka kira Yakin duniya na 2

Lallai sai kana da cikakkiyar masaniyar irin munafuncin da akayi da taimakon yammacin Turai aka goyawa Russia baya taga karshen Daular Usmaniyya ta Turkiyya, sannan daga baya suka juye suka hada kai da Amurka suka kafa wani abu da suka kira (NATO) don mallakar dukiya da karfin iko, sannan kasan sabon tsarin ayaga daga manyan kasashen Amurka da Turai din musamman ga kasashe masu dimbin ma’adinai da sauran arzuka, amma kasashe irin su China, North Korea, Cuba, Venezuela, Belarus, Iran da Russia suke matukar taka masu birki sannan ne za ka fi fahimtar dalilin dambarwar shekara da shekaru da ta hada China da Taiwan, Hong Kong da kuma tsakanin rikicin ilahirin Gabas ta tsakiya tsakanin su Iran, Syria, Yemen, Lebanon da Israela da rikicin Amurka da Cuba da Venezuela sannan ne za ka gane dalilin laqume Crimea da Russian tayi da kuma yanzu wannan rikicin na tsakaninta da Ukraine

Zan cigaba gobe in sha Allahu idan na samu lokaci

Naku

Dan’umma
Hassan Dandy

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here