NEMAN KOTU TA RUFE ASUSUN KANANAN HUKUMOMIN JIHAR KATSINA:

0

NEMAN KOTU TA RUFE ASUSUN KANANAN HUKUMOMIN JIHAR KATSINA:
….. RASHIN TAUSAYI DA RASHIN JIN KAI NE .

Sharhin Jaridun Katsina City News

Wani mai suna Ibrahim Lawal Dankaba, ya shigar da wata kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yana nema a rufe asusun ajiya na Kananan Hukumomin Jihar Katsina.

Dankaba shi ne Shugaban Karamar Hukumar Kaita lokacin gwamnatin PDP zamanin mulkin Ibrahim Shema.

Dankaba na daya daga cikin wadanda Hukumar EFCC ta gabatar a gaban Babbar Kotun Jihar Katsina a kan wasu kudade na Kananan Hukumomin Katsina bilyoyin Nairori.

Shi ne wanda ya shigar da kara a wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya yi korafin cewa gwamnatin Jihar Katsina ba ta biya wadanda aka zaba a Kananan Hukumomi, amma da zuwan gwamnatin APC ta rusa su kudaden da Kotun Koli ta umurci a biya su ba.

A iya binciken mu, gwamnatin Katsina ta biya duk shugabannin Kananan Hukumomi da mataimakansu da Kansilolin da aka zaba, kuma sun biya a bisa tsarin da tsohuwar gwamnatin PDP take biyan su da na gwamnatin Tarayya, kamar yadda jaridun mu suka ga takardun biyan, kuma ba wanda aka ba kudi a hannu, kowa ta Bankin da ya bayar aka biya shi.

Wadanda gwamnatin Katsina ta ki biya sune, Sakatarori da kuma Kansilolin nadaddu, wadanda ta ce su ba su cikin zababbu.

Yawan wadanda wannan tsarin ya shafa su 238 ne a duk fadin Jihar Katsina.
Wanda gwamnatin tace tana jiran fassarar babban kotun tarayya ta kasa kafin ta biya su ko karta biya

Dankaba, yana da ‘yancin zuwa kotu ya nemi hakkinsa, kamar kowane dan adam ko dan kasa, amma sanyawa a rufe asusun Kananan Hukumomi 34, wannan tsabar rashin tausayi da rashin jin kai ne.

Wannan yana nufin a hana ma’aikata kusan dubu 120 hakkinsu halak malak, wadanda ba su ji ba su gani ba!!?

See also  FG begins distribution of tractors to farmers in Kaduna

Kananan Hukumomin nan suna da Malaman makarantun Firamare sama da dubu 30 da iyalai da wadanda suka dogara da su.

Kananan Hukumomin nan suna da ma’aikata ciki har da na lafiya kusan dubu 30, wadanda su ma a nan suka dogara.

Ana ayyukan lafiya, ba da ruwan sha da sauran ayyukan jin kai da raya kasa, wadanda sama da mutane miliyan daya suka dogara da su.

Yanzu wadannan ayyukan duk sai su tsaya saboda bukatar nadaddun Kansiloli da Sakatarori 238?
wannan aikin na dankaba babu inda zai cutar da masu mulki ko masu rike da mukaman siyasa don bada kudin kananan hukumomi ake biyan su ba.
Wannan mummunan aikin zai cutar da talakawa ne a wannan lokacin da Talauci da rashin tsaro yayi ma al umma katutu.?
Ko jam iyyar PDP a jam iyance tana goyon bayan wannan aika aikar?
Ko a yaki na kasa da kasa ana la’akari da duk wani mataki da zai iya cutar da wadanda ba su ji ba su gani ba, amma son rai da neman daukar fansa na siyasa da rashin kishi ya sa za a cutar da miliyoyin al’umma.

Ya kamata jama’a su yi nazarin wannan da duk mai goyon bayan wannan rashin tausayi da rashin jin kai, domin tarihi da kuma in wata rana ya zo da wata bukatar zabe a gaban su .
Wannan wani mummunan shafi ake neman budewa a siyasar jahar katsina. Kuma ya kamata a lura a kumayi magana.

MATASHIYA
Wannan sharhin matsayin jaridun Katsina City News da jaridar Taskar Labarai da The Links News da ke bisa shafukan www.katsinacitynews.com. www.jaridartaskarlabarai.com. www.thelinksnews.com da ke bisa sauran shafukan sada zumunta.
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here