MASU NEMAN SARAUTAR WAZIRIN KATSINA SUN FITO
Ahmad Muhammad
@ katsina City news
An sami mutane uku da suka fara nuna sha’awarsu ta kasancewa a kan sarautar Wazirin Katsina bayan murabus din da Farfesa Sani Abubakar Lugga ya yi don kashin kansa.
Wadanda suka nuna sha’awar tasu sun hada da Sarkin Fadan Katsina; Abdulkadir Ismaila, wanda Wakili ne a Majalisar Sarkin Katsina, sai Abdul’aziz Isa Kaita, wanda Da ne ga Waziri Isa Kaita, dukkanin su biyun nan sun fito ne daga gidan Waziri Haruna. Sai na uku shi ne, Maliki Zayyad, wanda dan’uwa ne ga Waziri Hamza Zayyad daga gidan Waziri Zayyana.
Dama dai Katsina na da gidajen Sarauta guda biyu ne, haka ma Waziri gidajen biyu ne.
Gidan farko na Dallazawa ne karkashin Amir Umarun Dallaje, wanda ya karbo tuta daga Sakkwato a 1806/07. Na biyu shi ne gidan Sullubawa, wanda Turawan Ingila suka nada Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a 1906/07.
Sannan aka nada Waziri Haruna a 1906/07 a matsayin Waziri Katsina na farko, bisa amincewar Turawan Birtaniya ta hannun Sarkin Katsina Muhammadu Dikko.
Shi kuma Waziri Zayyana an nada shi a 1928, bisa amincewar Hukumar Mulkin da aka yi wa gyaran fuska a Arewacin Nijeriya.
Domin karfafa dangantaka Gidan Sarautar Dikko ya amince da aurarwa Dansa ‘Yar Waziri Haruna, inda daga baya ya gaje shi a matsayin Sarki Usman Nagogo. Ita ce mahaifiyar Marigayi Janar Hassan Usman Katsina.
Haka nan kuma, Sarki Usman Nagogo ya auri ‘Yar Waziri Zayyana, wanda dan sa yanzu ya zama Sarkin Katsina, Muhammadu Kabir Usman. Ita ce mahaifiyar Durbin Katsina, Aminu Kabir.
Saboda haka gidajen Sarautar Waziri guda biyun nan duka suna da alaka ta kut-da-kut da gidan Sarautar Katsina Muhammadu Dikko.
Jama’a dai sun zura idanu domin ganin daga wane gida za a zabo Wazirin Katsina.
Wannan dai zai karfafa tarihi na wadannan gidajen Sarauta biyu da suke da danganta ta tsawon lokaci.Sama da shekaru dari tare.1906 zuwa yanzu.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email.newslinks@gmail.com