Tsaunukan Kazaure “Mallam za ku siyi yalo?

0

_Tsaunukan Kazaure_ ⛰️

“Mallam za ku siyi yalo?” Dan dogon Yaron yayo kanmu tunda muka yi parking muka sassako daga mota

?

“Allah ya tsare, Allah ya kaiku gida lafiya” inji daya Yaron

“Kai yanzu baza kayi koyi da wannan Dan’uwan naka ba, kaga ya zabi Sana’a maimakon bara?” Na ce da dan gajeren yaron

Tun da zamu wuce Tsaunukan nan na Kazaure a hanyar mu ta zuwa Daura na ayyana a raina idan muka dawo sai na tsaya a wannan wuri saboda dalilai biyu, na farko naga dalar karas da yalo wadanda suka bani sha’awa inason yiwa manyan mutanen gida tsaraba, (saboda haka a dawowar mu dama daya daga cikin abokan tafiyar tamu Daurin auren da muka je Daura ya tsayar damu a dai dai Fago ya siyi kilishi, har a raina ina mamakin yanda Mallam Zakariyya zai sa kudinsa ya sai wai Kilishi) to amma dama nima din nayi niyyar zan tsaidamu siyen Yalo da Karas

Na biyu duk lokacin da zan wuce Tsaunukan Kazaure nakan qura masu ido in fantsama tunanin dadaddun abubuwan tarihin da wannan guri ya gani shekara da shekaru………………………

A jikin Tsaunukan nan ne Dan tunku ya fara tare maharan zinder akan hanyarsu ta zuwa kano yaqin farko, ance ma an gwabza qazamin fada da tawagar Sarki Aliyu Babba da ya turo a taryi Damagarawan a jikin Tsaunukan nan ne bayan nasarar kora “yan taryar Sarki Ahmadu Kuren Daga ya bi ta jikin Gadar Kazaure ta yankin Kunchi ya mamaye Qauyukan Malikawa ya nausa ya nemi shiga Kano ta Arewacin Birni ance daga nan ne a yankin Dawakin Tofa, Madaki yayi nasarar bashi baki ya koma

Damagarawa sun dade da fushin Kanawa tun rikice rikicen kasuwanci da mutanen Kanon a Qasar Zinder wanda ya kaiga yaqe yaqe tsakani

Har wala yau dai a shigowa ta biyu da Sarki Ahmadu Kuren Daga din dai yayi, a nan Tsaunukan Kazauren dai suka kuma sansani wannan karon sai suka nemi bullowa Birnin Kanon ta Gabas, ance har sun yi biji biji da Gezawa, an ta baiwa Sarki Aliyu Babba shawarar kada ya fita yaqin saboda Sarkin Damagaram yana da miyagun makamai daya gada daga Mahaifinsa Sarki Tanimu (tafiyayyun makamai daga larabawa da faransawa) amma dai ance ya nemi taimakon yan labanon da suke a Birni wadanda a lokacin ake da tabbacin har suna da bindinga irin ta Turawa

An dai yi yaqin kuma Damagarawan sunyi nasarar danna Kanawan da suka sheqa cikin Gari da gudu ciki kuwa harda Sarki Aliyun da kansa, ance Damagarawan sun matso har jikin Fagge suna shirin afkawa ilahirin Kanon ne sai Ahmadu Kuren Daga ya samu labarin ga faransawa can (wadanda ya fara rigima dasu a gida sun karo karfi daga Senegal sun dumfari Zinder) wannan ta tilasta masa qyale shiga Kanon da gaggawar komawa gida don tunkarar faransawan a yaqin da faransawan sukayi nasarar cinye ilahirin Zinder din da kashe Jarumin Sarki Ahmadu Kuren Daga, Wata ruwayar kuma na cewa lokacin da Sarkin Kano Aliyu ya koma Birni sai aka tattara Malamai aka dinga saukar Kur’anai kuma tasirin hakan ne ya hana Sarkin Damagaram din shiga Birnin Kano

Tarihi kuma ya nuna Kanawan sun fadi yakin ne sakamakon takun saqa da Masarautar ta Kano ta lokacin take da shi da Sarkin Musulmi Abdu Danyen Kasko, rikicin da yasa Sarkin Musulmin bai bada umarni ga Sarakuna maqwabtan Kanon su taho su taimaki Kanon ba !

Wannan guri dai harwala yau lokacin Sarkin Kazaure Muhammadu Mayaki a nan ya amshi bai’ar turawan da suka aiko masa da mubaya’a ko yaqi

Ana cewa tun daga Bida har Suleja har Zazzau, Kano har shiga Sokoto lallai kowa ya amsa kiran Sarkin Musulmi Attahirun Ahmadu na fafata yaqi da turawan maimakon mubayi’a amma banda Sarakunan Kazaure da Katsina, su kam salin alin suka miqa hannayen bai’arsu shiyasa har yau gidajen sarautar suna da martaba a idanun gidan sarautar Ingila.

Tsaunukan Kazaure kenan, ance cikin mutanen Barbushe, wani mutum makeri ana kiransa Kutumbi shine ya baro dutsen dala inda suke bautar tsumburbura ya nauso arewa farautar nama (dayake nama ya dade yana wahalar da bahaushe), ya dauki tsawon lokaci bai dawo ba, har iyalinsa suka bi hanya bazama nemansa

Ance a Tsaunukan nan na Kazaure suka iskeshi daidai kogin nan da ruwa ke gudu, shine ma wani daga cikinsu ya kalli gangaren Tsaunukan fili fetal sai yace “wannan (guri) kaman zaure” daga nan aka fara kiran gangaren tsaunin “kaman zaure” dayake a ilmin languages dama bahaushe yafi kowa lalacin harshe a hankali “kaman zaure” ta rikide ta koma *Kazaure !*

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here