MUTTAQA RABE DARMA YA FITO TAKARAR GWAMNAN KATSINA
muazu hassan
@ katsina city news
A yau litinin 7/3/2022 injinya Muttaqa Rabe Darma ya gabatar da takardun bukatar sa, na yin takarar gwamnan katsina a zaben 2023.
Ya gabatar da takardun ne a babban ofishin jam iyyar PDP dake titin zuwa Kano, jahar katsina.
Daga cikin wadanda suka shaida gabatar da wadannan takardun akwai Alhaji Abba ilah, shugaban jam iyyar PDP ta unguwar Muttaqa Rabe Darma.
Injinya ya gabatar da bukatar sa da wata Makala mai shafuka ashirin. Wadanda suka zayyano matsalolin katsina guda Goma da kuma hanyar da zai amfani dasu don magance su.
Ya kuma hada da wasu littafai masu kundaye biyar, wadanda ya rubuta, bayan daukar shekaru yana nazarin katsina da hanyoyin da za a bi ta kara samun daukaka da kuma cigaba.
Takarar ta injiniya muttaqa Rabe Darma zata tafi ne karkashin wani take mai suna da turanci. “Movement for greater katsina state”
Muttaqa Rabe tsohon Dan siyasa ne, tun zamanin NRC da SDP.ya taba rike mukamin kwamishinan wasanni da matasa a jahar katsina. Ya kuma rike sakatare a hukumar bada tallafin karo karatu na PTDF.
Shine shugaban dakin karatun PLBC dake katsina. Wadanda suke ayyukan ilmi da horas da sana o i.
Yana da digirin digirgir gangariya.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245
Email.newsthelinks@gmail.com