AIKIN KOFAR KWAYA KATSINA MIYASA MUTANEN UNGWANNI SUKE RAMI DA RUFE HANYOYINSU?

0

AIKIN KOFAR KWAYA KATSINA MIYASA MUTANEN UNGWANNI SUKE RAMI DA RUFE HANYOYINSU?

Daga Zahraddeen Sirajo Abbas

Miyasa Mutane suka kasa fahimtar cewa aikin Gadar Kofar Kaura da Kofar Kwaya a matsayin cigaban Karamar Hukumar Jahar katsina daga Najeriya baki daya, kafin Gwamnati ta fara shirin gudanar da wadannan aiyyukan babu irin zagi da cin mutuncin da ba’a yi wa Gwamnatin APC ta Rt Hon Aminu Bello Masari da sauran abubuwan da suka gudanar.

Bayan kazafi, karya da cin mutuncin da ake yi a kafafen sada zumunta, abun duk bai tsaya nan ba har akan dakko aiyyukan wasu jahohi a hada su da na Jahar katsina, ba don komai ba sai don a nuna gazawa da nuna cewa katsina ba’a yi komai ba, bayan kuma akwai abubuwa dayawa da aka gudanar wadanda ba’a yi su ba a wadannan jahohin.

Nayi tunanin Mutane Jahar katsina zasu dunga murna da nuna jin dadinsu akan irin yadda Gwamnatin Jahar katsina tayi kokarin ganin sharewa Al’umma hawayensu na samar da wasu hanyoyi na musamman wadanda zasu kawo saukin gudanar da harkokin yau da kullum.

Maimakon nuna jin dadi akan aiyyukan da ake gudanarwa a lokaci guda aikin Kofar Kaura da na Kofar Kwaya, sai kushe, karya, hassada, kiyayya, zage zage da maganganu na rashin dacewa da rashin sanin ya kamata, karshe ma wasu na fadin cewa ba wani cigaba da aiyyukan zasu kawo, wasu kuma na ganin ba ma cigaba bane.

A dukkan aiyyukan Gwamnati takan sanar kafin yi har ma ta bada shawarar bin wasu hanyoyin da take ganin cewa su ya kamata Al’umma su bi domin cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, sai dai har kwaliya ta kasa biyan kudin sabulu.

Ba lallai bane ace sai hanyoyin da Gwamnati ta bada umarni za’a bi ba, Mutane suna da damar bin hanyoyin da suke ganin sun dace kuma zasu yi masu saukin gudanar da harkokin yau da kullum, abun mamaki mutanen unguwar Kofar Kaura, sun rurrufe hanyoyinsu da Duwatsu, wasu sun tara kasa, wasu kuma sun ramin duk don kada a wuce.

Abun mamaki hakan ya sake faruwa a Kofar Kwaya, Mutane duk sun rufe hanya ba’a wucewa wai don kada a bata masu lunguna ko Gidaje da kura, Al’umma suna amfani da hanyar bayan Gidan Drugs domin zuwa Sabuwar Tasha ko katsina Central Market, ko Tashar Nato, ko Dalibai masu zuwa Makaranttun Polytechnic, Umyuk, FCE, Alqalam.

Mi zai sanya ayi Rami ko a zuba kasa a hanyar bayan Gidan Drugs, don kada Mutane su wuce, ya kamata Gwamnati ta daukin mataki akan irin wannan domin gujewa faruwar tarzoma.

Wani ganau ya tabbatar mani da cewa ma’aikatan Drugs sun fito da bindigogi sun sanya aka cire Slope domin kada Mutane su wuce da gurin bayan Gidansu, hanyar da ke kusa da inda ake sayar da Icce, wani ma ya tabbatar mani da cewa har sun dunga bugun Mutane a lokacin da ake gudanar da aikin.

Ina mai ba Al’umma hakurin jurewa abubuwan da zasu faru kafin bude hanyoyi, fara daga bin hanyoyin Kofar Gidajen Mutane da ma inda ba’a tunanin za’a bi, saboda aikin Kofar Kaura da Kofar Kwaya, sannan Gwamnati ta mai da hankali musamman ga masu yin Ramu da Tara kasa a hanyoyin da Mutane bi domin samun saukin wucewa.

Dan Jarida Mai Bincike
zahradeensirajoabbas@gmail.com
+2348065002570

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here