BATSARI DA WAGINI SUNYI SABBIN MAGADDAI.

0

BATSARI DA WAGINI SUNYI SABBIN MAGADDAI.

Ranar laraba 09-03-2022 akayi nadin sarautar Magaji Batsari a fadar mai martaba sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman.
Bikin nadin ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban, inda fadar ta cika makil ba masaka tsinke, ko ina ka duba dumbin masoya da masu fatan alheri ne.

Saurautar Magaji Batsari ta samo asali daga gidan Alhaji Ibrahim Uban dawaki wanda shine Magaji Batsari na farko, (1948-1984), watau ya kwashe shekaru 36 a gadon saurauta.

Sai Magaji Batsari, Musa Mai-aya, (185-1996), wanda ke nuna Shekar shi 11, akan gadon saurauta, kuma shi da ne ga Magaji Batsari Alhaji Ibrahim Uban dawaki.
Sai Magaji Batsari Ado, (1997-2022), wanda Allah yayi ma cikawa ranar alhamis 10-02-2022 da fatan Allah ya gafarta mashi. Magaji Batsari Ado ya kwashe shekaru 25 akan gadon saurauta, kuma shima da ne ga mariganyi Magaji Batsari Uban dawaki.

See also  PREPARING FOR A SUCCESSFUL NATIONAL AGRICULTURAL CENSUS!

Sai Magaji Batsari Bishir Ado Batsari wanda aka nada kamar yadda muka fada da fatan Allah ya taya shi riko, ya bashi ikon yin adalci.

A wani labarin kuma duk a ranar ta lahadi akayi nadin Muhammadu Sani Wagini, sarautar Magaji Wagini a fadar ta Masaurautar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here