GARIN SHIMFIDA YA FASHE

0

GARIN SHIMFIDA YA FASHE
……..Sakamakon janyewar sojoji
…….Mutane sun jikkata a kokarin gudu
Muazu hassan
Da safiyar yau alhamis 10/3/2022 mutanen garin shimfida dake karamar hukumar jibia suka ga Manyan motocin daukar kaya na sojoji, sun isa sansaninsu dake garin suna kwasar masu kaya.
Kafin azahar duk sojan dake sansanin sun bar in bar inda suke.
Wannan ya tada ma mutanen garin hankali suka fara tara yana su yana su suna barin garin .
Wannan turmutsin kokarin barin garin ya Sanya wasu yara bakwai sukayi muguwar galabaita a wata mota.har ana tsammanin wasu sun rasa ransu.
Bayan sojan sun bar garin na shimfida, wasu sun isa garin jibia, amma anga wasu kadan sun tsaya a garin gurbin baure.
Sansanin sojan shimfida yakai shekaru takwas a inda yake sai yanzu ya tashi ba tare da sanarwar wani dalili ba.
Manyan yan ta adda biyu,ke iko da yankin shimfida ..akwai sani Dangote sai kuma kacalla Ibrahim wani daya daga kwamandojin dan karami.
Yanzu haka yan gudun hijira daga garin na shimfida har sun fara kwararra garin jibia.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here