BARAYI SUN TAFI DA MATA DA YARA NA GARIN SHIMFIDA

0
95

BARAYI SUN TAFI DA MATA DA YARA NA GARIN SHIMFIDA
…Sun je garin sun washe shi.
…sunyi zaman sulhu da barayin
Muazu hassan
@ katsina city news
Barayin dake bangaren Ibrahim Dan gawo sun tare wasu Mata da yara guda Goma a kokarin su na gudu daga garin shimfida.
Matan suna tsakiyar tafiya da yaran su.sai barayin suka kewaye su. sai suka fitar da mace daya suka ce sun Santa daga kauyen Tagwaye take don haka tayi tafiyar ta.
Sun fada mata cewa ta shaida ma sauran jama a da yan shimfida suke fada, bada sauran mutane ba.
Barayin sun tafi da mata Tara da sama da yara kanana ashirin da wani magidanci a cikin su.mai suna kabiru.
Bayan fitar sojoji a garin na shimfida, barayi sun shiga garin sun kwashe komai a cikin garin.sun rika shiga gida gida. Daki Daki.abinci da kayan amfani duk sun kwashe.
Yankin na shimfida yana da manyan barayi guda uku.sani Dangote yana a tsaunin babare.ibrahim Dan gawo yana a bangaren Dumburun .sai Audu lankai yana bangare batsari da jibia.
Wani ganau da ya tsero daga garin yau asabar, ya shaida ma jaridun katsina city news, cewa Manyan barayin suna can suna tattaunawa mutanen dake yankin na shimfida akan su basu kariya su kuma su basu hadin kai.
Mai bamu labarin yace,mutanen yankin sun yanke shawarar zaman su lafiya,shine suyi sulhu da barayin nan.Tun da sojan Najeriya sun bayar dasu cikin sauki.
Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here