Karku bari a yi amfani da ku wajen yada jita-jita–Shugaban ƴan Jarida
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Shugaban yan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo, (internet) reshen jihar Kano, Hisham Habib, yayi kira ga ‘ya’yan kungiyar da kada su bari ayi amfani dasu wajan yada labaran karya marasa tushe ko yada jitajita duba da karatowar zaben shekara mai zuwa (2023).
Shugaban yayi Kiran ne lokacin taron ganawa da juna na musamman da kungiyar ta gabatar ranar Asabar a Kano.
Acikin Jawabin sa da ke dauke da sa hannun Sakataren kungiyar, Yakubu Salisu, Hisham yace Kiran ya zama wajibi duba da yadda kafafen yada labaran internet ke da tasiri a acikin al’umma, kuma kowa ke amfani da wayar sa wajan bibiyar me ke faruwa a duniya.
Kazalika ya ce ina kira da babbar murya ga ‘ya’yan kungiyar da su kasance kwararru akan aikin su ako da yaushe, sanan ya kuma ya yi kira ga al’umma da ma’aikatu da su tantance kafafen yadda labaran da za su yi mu’amula da su.