SABON GIDAN REDIYO A KATSINA MAI SUNA ALFIJIR

1

SABON GIDAN REDIYO A KATSINA MAI SUNA ALFIJIR
Suleman Umar
@katsina city news
Shahararriyar mai gabatar da shirin daga marubutanmu a gidan rediyon vision FM.hajiya Rabi at kabir Runka Zata bude sabon gidan rediyo mai suna ALFIJIR a cikin birnin katsina.
Mun samu tabbaci daga hukumar bada lasisin gidajen redio a Abuja cewar gidan rediyon ALFIJIR samu lasisi kuma har ya sawo kayan aiki.
Hukumar ta bashi damar ya fara gwaji daga Ranar jumma a 18/3/2022.
Binciken mu a katsina ya gano babban ofishin gidan rediyon yana bisa titin IBB kusa da gidan abincin katsina city restaurant dake wajen gari.
Wata majiya tace gidan rediyon mallakin Rabi atu kabir Runka ce .ita keda jari mafi yawa a ciki.
Munyi kokarin magana da Ita,amma abin yaci tura don wayarta na kadawa amma bata dauka ba.mun kuma aika mata sakon rubutun wayar hannu ba amsa.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here