AN AMINCE WA KWALEJIN KULA DA LAFIYA TA KATSINA TA GABATAR DA KWASA-KWASAI 4

0

AN AMINCE WA KWALEJIN KULA DA LAFIYA TA KATSINA TA GABATAR DA KWASA-KWASAI 4

SANARWA

Kwalejin Kula da Lafiya da Kimiyya da Fasaha ta Katsina (Katsina State College of Health Sciences and Technology), na sanar da al’umma cewa, Hukumar kula da Ilimin Kimiyya da Fasahar {ere-}ere ta {asa (NBTE), ta amince mata ta gudanar da kwasa-kwasan Diploma ta kasa kamar Haka.

1. National Diploma Nutrition and Dietetics (ND NUT & DIT)

2. National Diploma Health Information Management (ND HIM)

3. National Diploma Dental Therapy (ND Dental Therapy)

4. National Diploma Environmental Health (ND Environmental Health).

Saboda haka duk wanda ke bukatar daukar daya daga cikin wadannan kwasa-kwasan sai ya cika takardar JAMB, domin kuwa wanda ya sami abin da ake bukata ne kadai zai sami gurbin shiga Kwalejin.

Wanda ya samu yawan makin da ake bukata a JAMB ne kadai za a ba gurbin karatu a zangon karatu na 2022/2023.

Sa Hannu:
Aliyu Bala Kurfi, MCPN
A madadin Magatakardan Kwalejin
Fassara. Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here