Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce Jam’iyar PDP ba ta tunanin baiwa wani ɓangare na ƙasar nan takarar shugaban ƙasa a 2023.
Tambuwal ya faɗi hakan ne ga manema labarai yayin da ya kai wa tsofaffin shugabannin soji na ƙasar nan, Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar a gidajensu da a Mina, Jihar Naija.
Tambuwal, wanda ya ke takarar shugabancin ƙasa, ya ce rabon takara na shiyya-shiyya bai taɓa zama wani abin baiwa muhimmanci ga jam’iya ba a ƙasar nan tun 1979.
Abin da jam’iya ta ke yi shine ta a jiye kujerar ga ƴan takara in yaso mai rabo ka ɗauka.
A cewar sa, “fitowar tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo da ga ya kin Kudu-maso-Yamma a 1999, wani mataki ne a ka ɗauke shi da gaiya domin magance wata matsala da ta taso sakamakon rusa zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993.”
Gwamnan ya ce yanzu abin da ke gaban PDP shine yadda za ta ci zaɓen 2023, inda ya ce ƙasar nan na matuƙar bukatar shugaba mai jajirce wa wajen gyaran ƙasar nan ba wai ɓangaranci ba.