Kwamitin da jam’iyyar APC ta ɗora ma alhakin tantance masu neman tsayawa takarar muƙaman shuwagabanni jam’iyyar na kasa, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, yana ci gaba da aikin shi kamar yadda aka tsara.
Ya zuwa yanzu, kwamitin ya gama tantance masu neman tsayawa takarar Shugaban Jam’iyya, Muƙaddashin shi, Mataimakan shi na shiyyoyi da kuma Magatakardan jam’iyyar. Ana kuma ci gaba da tantance sauran masu neman tsayawa takarar wasu kujerun daban-daban.
Daga Jihar Katsina Kuma, an tantance Dantakarar kujerar National Legal Adviser Barrister Ahmad Usman Al-marzuk Kwamshinan Shari’a na Jihar Katsina, Kwamitin ya yabama shi akan kwarewarsa akan Shari’a Duba da takardunsa da suka gani.
Wannan Kwamitin yana cike da manyan ya’yan jam’iyyar wanda suka haɗa da tsohon kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya Honorabul Oladimeji Bankole, tsohon Gwamnan Jihar Borno Alhaji Maina Ma’aji Lawan, Werinipre D. Seibarigu, Sanata Aishatu Dahiru Binani.
Sanata Ibrahim Hassan Hadeja, Alhaji Abdullahi T. Gwarzo sai kuma Sakataren kwamitin Barista Emmanuel Chukwuemeka da sauransu.
Kwamitin na gudanar da aikin nasa a gidan Gwamnatin Jahar Katsina Dake Asokoro Babban Birnin tarayya Abuja a yau laraba 23/03/2022 karkashin Shugaban Kwamitin na Kasa Gwamna Aminu Bello Masari CFR.
Addu’ar mu Allah Yasa a gama lafiya, ya yi mamu zaɓi mafi alkhairi kuma Ya tsare mana jihar mu da ƙasar mu baki ɗaya.