“Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya bayyana cewa APC za ta ci gaba da zama kan mulki saboda ta kyautata tare da share hawayen ‘yan Nijeriya.

“Malam Isah Yuguda ya ce, manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar ko kusa ba za su iya ja da Jam’iyyar ta su ta APC ba saboda karfin da take da ita da rawar da ta taka wajen share hawayen ‘Yan Nijeriya.

“Malam Isa Yuguda, ya bayyana haka a wata hirar bidiyo da BBC Hausa suka wallafa a shaginsu na Internet.

“Tsohon gwamnan ya ce, za su karya lagon su Atiku Abubakar da jam’iyyar hamayya ta PDP kuma sun shirya tsaf domin jaddada nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zabukan 2015 da 2019.

See also  DR DIKKO RADDA YA RUFE GANGAMIN YAKIN NEMAN ZABEN SA A MALUMFASHI

“Yuguda, a cikin hirar tasa ya bayyana janyewarsa daga neman shugabancin jam’iyyar APC na kasa, ya ce ya janye daga takarar saboda jam’iyyar ta kebe kujerar ga shiyyar arewa ta tsakiya shi kuma ya fito ne daga arewa maso-gabas.

“Ya kuma ya bayyanawa duniya cewa yanzu ya koma neman mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar arewacin Najeriya.

© KBC Hausa News.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here