AIKIN GADAR KOFAR KWAYA YA TSAYA CAK…labari cikin hotuna.
@katsina city news
Yau jumma a 25/3/2022 sati biyu kenan da tsayawar aikin gadar kofar kaura cak.
Ziyarar da muka kai yau, babu ko shebur na kamfanin dake aikin.sun tare hanyoyin wucewa sun Gina wani katon Rami sun kuma bar wajen aikin.
Kamfanin dake aikin Traictra ya kwashe duk wani kayan shi daga wajen aikin sai wani wawaken Rami da ya bari.
Al ummar katsina na azabtuwa da wannan aikin. An bar sako masu ruwan sha don kar yayi barna ga masu aikin,
Mun rasa Wanda zamu yi magana dashi akan yadda kamfanin ya kwashe kayan shi a wajen aikin.
Mun aika sako da Shugaban kamfanin na traictra na katsina babu amsa.
Haka ma kwamishinan ayyuka na jahar katsina Wanda aikin ke karkashin sa.yaki daukar waya ya kuma ki bada amsar sakon wayar hannu da muka aika masa.
Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245