Tsohon ɗan takarar gwamna a Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyar PDP a 2019, Jafar Sani Bello, ya ja hankalin uwar jam’iyar ta kasa da kasa ta kuskura ta amsa kiraye-kirayen cewa a rushe shugabannin jam’iyar a jihar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun bayan da tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo PDP daga APC gabannin zaɓen 2019, sai jam’iyar ta dare gida biyu, da ɓangaren shi Kwankwason da kuma na tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Wali.

A kwanan nan ne kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyar a Kano ke kira ga uwar jam’iyar ta ƙasa da ta rushe shugabancin jam’iyar a jihar, bisa zargin cewa a ƙarƙashin ikon Kwankwaso su ke.

To shine, a wata wasiƙa da ya aike wa uwar jam’iyar a ranar 24 ga watan Maris, Bello ya suffanta kiraye-kirayen rushe shugabancin jam’iyar a matsayin yi wa dimokaraɗiyya da kundin tsarin mulkin ƙasa hawan ƙawara.

Jafar Sani-Bello ya ƙara da cewa rushe shugabancin jam’iyar a bisa dalilin cewa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa NNPP, wannan ba haujja ba ce kuma ya saɓa da hakkin ƴancin ɗan ƙasa da ya ke ɗauke a sashi na 4 (40) na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999.

See also  WANI DAN KATSINA YA ZAMA DAN MAJALISAR TARAYYA A KANO.

Sannan ya ƙara da cewa idan ɓangaren Aminu Wali su ka zargi Kwankwaso da yi wa jam’iya zagon ƙasa, to ai su ma su na da kashi a gindi a kan hakan.

A cewar Sani-Bello, a zaɓen gwamna na 2019, ta tabbata ɓangaren Wali sun taimaka wa jam’iyar APC, inda ya ƙara da cewa bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dawo mulki a karo na biyu, ya biya shi Walin da kujerar Kwamishina, inda ya naɗa Sadik Aminu Wali a matsayin Kwamishinan Ruwa.

Ya kuma ƙara da cewa haka shima Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda ƙusa ne a ɓangaren Wali, a ka baiwa surikin sa muƙami a gwamnatin ta Ganduje.

Ya kuma na hankalin uwar jam’iyar cewa shiga wata jam’iya fa ra’ayi ne na mutum kamar yadda ya ke a sashi na 2(1) da ka sashi na 8(4) a kundin dokoki na PDP.

Daga nan ne sai Sani-Bello ya gargaɗi uwar jam’iyar a kan ɗaukar wannan mataki, inda ya kuma yi kira gare ta da ta yi gaggawar sulhunta rikicin da ke cikin jami’ar a Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here