AN KONE RIGUNAN MUSTAFA INUWA A ABUJA

0

AN KONE RIGUNAN MUSTAFA INUWA A ABUJA
@ katsina city news
Wasu matasa wadanda sukayi ikirarin daga karamar hukumar batsari suke, sun kone riguna da hulunan dakta Mustafa inuwa sakataren gwamnatin katsina kuma mai neman jam iyyar APC ta tsayar dake takarar gwamnan katsina a zaben 2023.a taron APC Abuja
Wani bidiyon da jaridun katsina city news suka gani Wanda ke yawo a bisa shafukan sada zumunta sunga wadannan matasa suna batanci ga Mustafa inuwa da kone kayayyaki masu dauke da hotunan sa.
Wani matashi a bidiyon yace sun fito daga batsari ne ta jahar katsina.
Jaridun taskar labarai da katsina city news basu iya gano koda mutum daya da suka nuna wancan fushin nasu ba domin jin dalilin su na yin haka.
Bidiyon ya kumshi kalaman batanci .Wanda a kaidar aikin jarida ba zamu iya saka shi a shafukan mu ba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here