EFCC Ta Gurfanar Da Dan Ƙasar Indiya Saboda Cek Na Miliyan 70 Na Karya

Hukumar EFCC ta gurfanar da wani dan kasar Indiya Yuvraj Kumar Mehra a gaban mai shari’a Olanrawaju Majekobe na kotun jihar Ogun akan tuhuma takwas mai alaka da hadin baki da bayar da cek na karya na kudi miliyan saba’in.

An gurfanar da shi ne tare da kamfaninshi Dolphin Steels Nigeria Limited saboda yaki biyan kamfanin raba wutan lantarki na Ibadan kudin na wuta da aka baiwa kamfanin nashi inda bincike ya gano cewa ya biya kudin cek na miliyan dari da ashirin da biyar na karya daga daga watan Oktoba 2, zuwa Oktoba 3, 2018.

See also  BUƊE CIBIYAR SADARWA TA GAGGAWA (112) NA BUKATAR SABON LALE DA KULAWA

Bayan kamfanin raba wutan lantarki ya matsa masa ne ya biya wani kaso na kudin.

Ya dai musanta laifin nashi inda mai shari’a ya bayar da belinshi akan kudi miliyan hudu da dubu dari da masu tsaya mishi da zasu ajiye miliyan biyu da dubu hamsin kuma dole su kasance masu filaye a jihar ogun, kuma dole ya ajiye fasfo din shi tare da kotu. Inda ya daga sauraren karar zuwa Mayu 18, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here