MAJIGIRI ZAI TSAYA TAKARAR GWAMNA A JA IYYAR PDP?

0

MAJIGIRI ZAI TSAYA TAKARAR GWAMNA A JA IYYAR PDP?
muazu hassan
@ katsina city news
Akwai yiyuwar shugaban jam iyyar PDP na jahar katsina, Alhaji salisu Yusufu majigiri ya tsaya neman takarar gwamnan katsina a zaben 2023 a jam iyyar PDP.
Wata majiya mai tushe tace wasu wasu daga cikin masu fada aji na jam iyyar sun yanke shawarar kiran majigiri domin yayi wannan takarar.
Majiyarmu ta tabbatar mana cewa, tsohon gwamnan katsina Alhaji Ibrahim shema ya gana da wasu masu fada aji na jam iyyar a gidan sa na Abuja, Kaduna da Dutsinma duk a zaman an yanke shawarar mara wa majigiri baya ya tsaya takara.
Munyi magana da wasu daga cikin wasu masu fada ajin, sun tabbatar mana da gaskiyar maganar.
Sunce majigiri shine mafi cancanta PDP ta tsayar,domin yana da duk abin da Dan takara ke bukata.
Sai dai har zuwa rubuta rahoton nan, Majigiri bai sayi fom na tsayawa takara ba.bai kuma nuna sha awar hakan a bayyane ba.
Munyi kokarin magana dashi, bamu samu ba.
Kawo yanzu mutane uku suka sayi fom a jam iyyar PDP .sanata Yakubu lado Danmarke.shehu Inuwa imam.sai Ahmad Aminu yar adua.
Jam iyyar PDP zata rufe sayar da fom din takarkarin ta a ranar 1/4/2023.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here