YAN BINDIGA SUN BA MUTANEN BATSARI KWANAKI BAKWAI

0

YAN BINDIGA SUN BA MUTANEN BATSARI KWANAKI BAKWAI
…..Ayi sulhu ko su afka masa
…..sakon su ga sarkin Ruma
Daga misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news

A ranar asabar 26-03-2022, ƴan bindiga suka bada wa’adin mako ɗaya ga mutanen Batsari ko su sake kai hari garin.
Wani makusancin Sarkin Ruma hakimin Batsari ya bayyana mana cewa ƴan bindiga sun bugo ma sarki waya ranar asabar da safe, inda suka ce masa a daina taɓa mutanen su, kuma a sasanta dasu, idan ba’a yi masu haka ba to zasu kawo hari Batsari nan da mako ɗaya.
Binciken mu ya nuna cewa a ranar alhamis 24-03-2022 wasu fulani su ukku maza biyu mace ɗaya suna cikin motar haya zasu je Katsina wajen hidimar shirye-shiryen tafiya Makka sai wani da ake zaton jami’in tsaro ne yasa aka kama su aka ɗaure mazan, kashe gari suka ce ga garin ku nan.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilin su na cewa zasu ɗauki mataki idan ba’ayi sulhu da su ba.

Haka kuma, wani cikin ƴan fadar sarki ya shaida ma wakilin mu cewa, yau da safiyar lahadi 27-03-2022, wani da yaso mu sakaya sunan sa, yazo fadar sarki yayi gaisuwa sannan ya bayyana ma sarki cewa, ina ɗaya daga cikin mutanen dake zuwa inda ake haƙar ma’adanai dake ƙauyen Nahuta ta ƙaramar hukumar Batsari, muna cikin hada hadar aiki sai ƴan bindiga su kimanin talatin suka zo ɗauke da miyagun makamai suka tara mu suka ce kowa ya ware ƴan garin su domin suna so su gane mutanen kowane gari.
Mutane sun tsorata har wasu sunyi raunuka wajen gudu, sai sukace duk ɗan Batsari ya bar wajen, domin an kashe masu mutane a Batsari kuma basu yi laifin komai ba. Sannan suka ce ga saƙo su faɗi ma Sarkin Rumah, suna so yasa a tada ƴan civilian JTF daga Batsari, kuma a sasanta dasu a barsu su riƙa shiga gari suna yin harkokin su tunda dai sun shafa ma Batsari lafiya basa yin wani ta’addanci a garin, tsallakewa suke yi, amma su anƙi a bar su. Idan kuma ba haka ba, to zasu kawo hari nan da mako ɗaya.

See also  "YAN BINDIGA SUN ZAMA SARAKUNA A YANKIN BATSARI 

Irin wannan iƙirarin sun taɓa yin shi kuma suka cika, domin lokacin da suka kawo hari Unguwar Katoge ta Batsari sai da suka bugo waya sukace zasu zo, kuma sun shigo, sunyi abinda sukayi na kashe mutum ɗaya da garkuwa da mutane fiye da ashirin waɗanda suka kwashe watanni shida a hannun su.
Yan batsari na fatan wannan karon hukumomi zasu ɗauki matakin da ya dace domin daidaita al’amurra.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here