JARIDAR TASKAR LABARAI DIKKO RADDA, KAR KA SAUKA AKAN KUJERARKA

0

SHARHIN: JARIDAR TASKAR LABARAI
DIKKO RADDA, KAR KA SAUKA AKAN KUJERARKA!,ll

Wannan sharhi ne na matsayar jaridar TASKAR LABARAI a kan kudurin takarar Dikko Umar Radda da yanzu yake rike da mukamin Shugaban Hukumar Tallafawa Kananan Masana’antu ta Nijeriya (SMEDAN), mukamin da a doka zai ci gaba da rikewa har zuwa wasu shekaru masu zuwa.

Mun rubuta wannan sharhi ne bisa kishin Katsina da kuma hangen me zai iya zuwa ya dawo da kuma kyakkyawan zaton da muke a kan Dikko Radda a kan kishinsa na Katsina.

An kafa shafin jaridar TASKAR LABARAI a shekarar 2016 a bisa shafin www.jaridartaskarlabarai.com da sauran shafukan da ke kan yanar gizo. Shafin ya fi ba da karfi ne a kan labaran harkar tsaro, cin hanci da rashawa da kuma kyakkyawar dimokaradiyya.

Shafin shi ne ya fito wa duniya halin da Jihar Katsina da Arewa maso Yamma ke ciki a kan halin tsaro da hasashen lamarin zai kara munana a gaba.

A shekarar 2018 babban Editan shafin ya rubuta wata budaddiyar wasika a kan halin tsaro da Jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna za su fada in ba a yi hankali ba. Manyan jaridun kasar nan sun yi labari a kan wasikar. Kuma duk wanda ya shiga yanar gizo zai gan ta. Abin da ya yi hasashe a shekarar 2018 shi ne yake faruwa a yanzu.taken wasikar itace; insecurity: Act before it is too late..katsina publisher

A zaben 2019 shafin ya dau matsaya cewa, takarar Yakubu Lado a jam’iyyar PDP ba ta dace da ci gaban Katsina ba a lokacin.
A lokacin jaridar ta dau mataki da matsayar fadakar da jama ar katsina akan karsu zabi jam iyyar PDP a zaben gwamna.saboda kuskuren tsayar da Yakubu lado da sukayi a matsayin Dan takarar gwamna a lokacin. Sunyi sharhi da Rubutu masu yawa akan haka.
Da aka sace yan daliban makarantar kimiyya ta Kankara.jaridarce, farko da ta bayyana ma duniya, wane Dan ta adda ne, ya jagoranci harin.sunansa da tarihin shi.Da wannan bayanin aka hau aka gano shi aka fara magana dashi.Har Allah ya kubuto yaran baki daya babu ko kwarzane.

Dokar zaben 2022, wadda yanzu ake dambarwa a kanta a kotu, ta ce, duk wanda zai yi takara ya ajiye mukaminshi. Uwar jam’iyyar APC ta ba bai wa duk ‘ya’yanta umurnin duk mai niyyar takara ya shirya ajiye mukamin siyasa da yake rike da shi.

Ada akwai mukamai da yawa da ke hannun ‘yan Jihar Katsina da suka hada da NPA, NHIS, FMBN, FHA da sauransu, yanzu sun sullube, wasu kuma lokacin da aka deba masa ba su kare ba irin su FERMA, SMEDAN da sauransu.

SMEDAN: Wannan Hukuma tana daya daga cikin masu muhimmanci masu taimakon al’umma a kasa. Matashi dan Katsina mai kishi da aiki tukuru ke jagorantar ta shi ne Alhaji Dikko Radda, Gwagwaren Katsina.

A matsayar jaridar TASKAR LABARAI, in saboda da yi wa al’umma aiki ne, in saboda kishin al’ummar Katsina ne, in saboda cigaban kasarmu ne Nijeriya, Dikko Radda kar ya ajiye mukamin da yake, da sauran shekaru yana aiki, saboda takara.

Duk shekara Hukumar SMEDAN na da kasafin kudi sama da naira biliyan 70. Ban da mu’amala da manyan hukumomin duniya, kamfanoni da ‘yan kasuwa, wanda kasafinsu sai an daddale.

A matsayarmu, wanda ke da wannan damar ba shi da bukatar ya ajiye wannan kujerar domin takara. Kamata ya yi ya ci gaba da wakilci mai kyau na Katsina, Hausa Fulani, da arewacin Nijeriya.

A iya abun da muka sani, wanda bayaninsu ba na jarida bane, a yanzu sai dai ko in ta kama dole. watakila a bisa kaddarar rayuwar Dikko Umar Radda akwai, ya zama Gwamnan Katsina (Allah shi ne masanin gaibu). Daga lissafin da ke tafiya,Wannan kaddarar ba a shekarar 2023 take ba.

Muna ba Dikko Umar Radda shawara ya jinjina kafin ya ajiye mukaminsa ya fito takara. Zai yi abin da tarihi zai rika tunawa da shi. Zai kuma yi abin da zai iya shafar tarihin rayuwarsa a siyasance.

Wannan matsayar shafin jaridar TASKAR LABARAI ce, kuma a kan ta za mu tafi har zaben 2023.

Shafin taskar labarai yana a
Www.jaridartaskarlabarai.com
Facebook; jaridar taskar labarai
Twitter @ taskar labarai
You tube .taskar labarai TV.
07043777779 (WhatsApp).08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here