Ministan jinƙai Hajiya Sadiya Umar Faruƙ tayi kira ga matan da suka amfana da shirin da suyi amfani da kuɗin da gwamnatin tarayya ta basu domin inganta rayuwar su da ta iyalan su.

Sadiya tayi wannan kira ne yayin da take ƙaddamar da shirin bada ƙudi ga matan karkarar a jihar Gombe a ƙarshen shekarar 2020.

Ministan jinƙai tayi fatan matan suyi amfani da kuɗin domin inganta ƙananan sana’o’in su wanda kayi kawo cigaban tattalin arziƙin ƙasa.

Ta ƙara da cewa shirin bada ƙuɗi ga matan na ɗaya daga cikin ƙoƴarin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, na tsamar da ƴan ƙasa daga ƙangin talauci.

Daga ƙarshe ministan ta ƙaddamar da raba kuɗin na naira dubu ashirin ga kowannen su .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here