A Rana Mai Kamar Ta Yau 19 Ga Watan Afrilu A Shekarar 1969 A ka Daura Auren Shugaban kasar Nijeriya janar Yakubu Gawon Tare Da Victoria Hafsatu Zakari, Yakubu Gowon Ya zama Shugaban kasa yana Saurayi Mai Shekaru 31, A 1966. Amaryar Tasa Ma’aikaciyar Jinyace Yar Asalin Zariya. An Daura Auren Ana Tsaka Da Yakin Basasar Najeriya, Wanda Ya Janyo Cece-kuce A Tsakanin Yan Kasa. A Cocin Christ Church Cathedral, Lagos A ka Daura Auren.
Victoria Hafsatu Zakari Gawon Tayi Tasiri Sosai A Gwamnatin Mijin Nata, Domin Itace Tasa Gwamnati Ta Daidaita Albashin Ma’aikatan Jiyya Yan Kasa Da Yan Kasashen Waje Dake Aiki A Najeriya.