DANLAMI KURFI YA FICE DA GA APC YA KOMA PDP

0

DANLAMI KURFI YA FICE DA GA APC YA KOMA PDP
muazu hassan
@ katsina city news
Shararren Dan kasuwar nan mai kishin jihar katsina Wanda ya mallaki gidan saukar Baki na Hayyat Regency..katsina da Daura.da kuma wani sashen bada wutar lantarki ta Nepa .karkashin kamfanin DMkurfi ya fice daga jam iyyar APC zuwa PDP.
Wata majiya mai tabbas ta tabbatar mana da Alhaji Danlami kurfi ya koma jam iyyar PDP har ya sayi fom na neman takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kurfi da Dutsinma a jam iyyar PDP.
Danlami kurfi ya tabbatar ma da jaridun katsina city news cewa lallai ya chanza sheka daga APC zuwa PDP bisa bukatar mutanen shi da saboda su yake siyasa.
“Na tattauna da mutane na,sun ce mu bar jam iyyar kawai zuwa PDP ni kuma domin su nake siyasa, shi ya Sanya na chanza”
Danlami kurfi,tsohon dan majalisar dokokin jahar katsina ne,kuma tsohon Dan majalisar tarayya Wanda ya wakilci kurfi da Dutsinma .
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here