FAROUK JOBE :YA AJIYE MUKAMINSHI DON TAKARAR GWAMNAN KATSINA.

0

FAROUK JOBE :YA AJIYE MUKAMINSHI DON TAKARAR GWAMNAN KATSINA.
Muazu Hassan
@ katsina city news
Alhaji Farouk Lawal Jobe Kankara, kwamishinan kasafin kudi na jahar katsina ya ajiye mukamin shi domin neman tsayawa takarar gwamnan katsina. Kamar yadda jama a suka Nemi ya fito.
Jaridun katsina city news sun ga wasikar da ya rubuta ma gwamnan katsina tun 31/3/ 2022 inda a cikin yayi bayani, mayar da albashin sa na watan March 2022 da kuma a ajiye mukamin shi daga ranar 31/3/2022.kuma wasikar ta nuna tun a ranar aka amshi wasikar.
A wasikar Farouk jobe yayi Godiya ga damar da gwamnan katsina ya bashi na bada tashi gudummuwar a jahar katsina.ya kuma kara samun darasin tafiyar da aiki da rayuwa.
Farouk jobe kwararren masanin harkar kudi ne da aikin Banki. Wanda ya rike mukamai daban daban kafin ya ajiye aiki.A tarihin siyasar shi bai taba wata jam iyya ba sai APC.
Ya mallaki makaranta mai zaman kanta wadda tana cikin makarantu masu tsari da koyarwa tukuru a jahar katsina.
Ya zuwa Rubuta wannan Rahoton shi kadai ne Dan takarar gwamna da ya fito daga shiyyar funtua.ya zuwa rubuta rahoton nan, Mutane biyu sun nuna aniyarsu daga shiyyar Daura.mutane hudu daga shiyyar katsina. Daga shiyyar funtua kuma mutum daya shine Farouk lawal jobe.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here