MARTANIN JAM’IYYAR APC A KARAMAR HUKUMAR RIMI

0

BA NI NA KASHE ZOMAN BA…..

MARTANIN JAM’IYYAR APC A KARAMAR HUKUMAR RIMI…….

Tare da Abdulrahaman Aliyu

Rukunin Jaridun Katsina City News, kamfani ne mai zaman kansa kuma kamfani daya tilo a jihar Katsina da ya cika dukkan wasu sharudda na kasancewarsa kamfanin jarida mai aiki a yanar gizo da kuma buga mujallu da jaridu a takarda.

Kamfani ne da bai tsaya kan kare muradan wata gwamanati ko rukunin wasu mutane ba, ya na aiki ne kai tsaye ga al’umma ta fuskar bincike da nazari kan mabambata abubuwa.

Rashin sanin yadda aikin jarida yake ne danganta kamfanin da wani mutum ko wata jam’iyya ko kungiya.

Zamowar ka ma’aikaci a kamfanin ba hakan na nufin kare muradan da kake so ba ne ko kuma bayyana ra’ayin kashin kanka a shafukan jaridun ba.

Kwanan baya jaridun sun fitar da wani rahoto da ya shafi jam’iyyar APC a karamar hukumar Rimi, wanda ya tayar da hazo kan yadda wasu ke wa jam’iyyar zagon kasa a karamar hukumar.

A daya daga cikin martanin da wani jigo a jami’iyyar ya mayar ta hannun wata jarida ya bayyana abubuwa da yawa tare da zarge-zarge da kuma kare kai kan hasashen da yake kamar an shirya rubutun domin shi ne.

Daga cikin zargin da ya yi ya bayyana tarihi da kuma yadda karamar hukumar Rimi ta rasa wakilci na majalissar tarayya tun bayan 1999.

Duk da dai tarihin ya tsaya ne ga jam’iyyar PDP wadda kuma ba ita ke mulki ba a yanzu.

Haka kuma, ya kara mana haske kan yadda duk wasu masu ruwa da tsaki da jigajigan jam’iyya mai mulki a karamar hukumar Rimi suka sake juya baya ga dan takarar da jam’iyyar ta fitar daga Rimi, da kuma irin namijin kokarin da su hudu zuwa uku kadai suka yi na ganin kujerar bata sullube ba amma Allah ya yi nasa ikon.

Ko shakka babu a nan wajibi duk mai kishin karamar hukumar Rimi ya yaba maku matuka, duk da dai binciken da jaridar nan ta yi ya gano cewa a lokacin sanya bakinku ne ya harzuka da yawa daga cikin EXCO din suka aikata abinda su ka yi. Amma ni a bagarena ina matukar yi maku jinjina da yabawa.

Game da taron masu ruwa da tsaki da aka kalubalanci rubutun da jaridar nan ta buga kuwa na cewa duk mai kishin Rimi ya san wadannan mutane talatin da aka wassafa ginshikai ne da in ana maganar jam’iyyar APC a karamar hukumar Rimi to wajibi ne a bar su su taka.

Korafin rubutun shi ne irin wannan taro kamata ya yi ko ba aga shugaban masu ruwa da tsaki ba na karamar hukumar kamata ya yi ace da sa hannunsa aka gudanar da taron ko kuma Yana daya daga cikin mutane uku da aka gayyata a mazabar sa, duba da cewa ba a shugabanci a cikin shugabanci, wanda hakan ka iya kawo babbar baraka da zata zama barazana ga zaman lafiyar jam’iyyar APC, musamman irin kallon da wadanda ba a gayyata ba za su rika yi wa taron na ganin kamar an ware su, daga nan sai su fara kiran nasu taron, wannna shi ne kawai hange da nazarin rubutun da ya gabata ke nusarwa a kai.

A martanin an yi korafin cewa wanda aka ce ma su ya yi rubutun ko kuma suke zargi, su ne suka yi hanyar zuwa garinsu kuma su suka gina masallacin juma’ar garin su da Islamiyyar garinsu.

Ko shakka babu wadannan kalamai sun yi nauyi ga wanda ake zargi ba tabbatarwa ba, a nan ana son a ci mutuncin zuri’arsu ne baki daya a nuna cewa kafin su zama shugabannin al’ummar wannan yankin musuluncinsu ma kadan ne, tunda basu da masallacin kuma basu da makarantar koyon addini.

Sai dai shi aiki irin wannan da ake ikirarin an yi masu ai ba abun alfahari ba ne ko tunkaho tun da nauyi ne da mutum ya dauka ya safke, haka kuma riba ma aka samu tun da ba da kudin aljihu aka gabatar da aikin ba, an yi amfani da kudin gwamnati kuma hakki na wadannan mutane, kuma ko shakka bana yi sai an ci riba.

Duk da haka dai muna godiya matuka ga wadanda suka samar mana da hanya da kuma gina mana masallatai da asibitoci da Islamiyyyu Allah ya saka masu da alherinsa amin.

Daga karshe na so a ce a martanin an bayyana dalilin da ya sa wani kansila daya da ba a samu damar ganawa da shi ba abin da ya hana shi zuwa.

Kodayake ba laifi ba ne dan ina jam’iyyar APC na buge da tallata ayyuka jam’iyyar adawa a cikin zantuka na.

Ina fatan zamu rika tantance abubuwa yadda suke da yadda ake aiwatar da su kafin dora zargi ko martani kan wani abu. Allah ya shige mana gaba ya albarkaci jagororinmu da mu kanmu tare da karamar hukumarmu baki daya. Allah ya hada kanmu ya wargaza duk mai son ganin mun wargaje.

Abdulrahaman Aliyu Marubuci ne na musamman a rukunin jaridun Katsina City News, Taskar Labarai, The Links News.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here