Am bayyana Qs Mannir Yaqub a matsayin mutum mai ilimin da zai iya kyakkyawan jagoranci idan Allah ya bashi Gwamnan Katsina.

Khadijah Abubakar @Jaridar Taskar labarai

Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai akan takarar tsohon Kwamishinan Noma kuma mataimakin Gwamnan jihar Katsina QS Mannir Yakubu.

Taron na manema labarai a karkashin jagorancin Ibrahim Jikamshi yayi karin kaske akan dalilin kiran taron, da Manufar taron.

Jikamshi yace “mun kiraku ‘yanjarida saboda mahimmancin ku, kune zamu bayyana wa Manufar mu da yunkurin mu, ku kuma ku bayyanawa al’uma.”

Jikamshi ya jaddada dalilin taron ba don komi ba sai don bayyana Mataimakin Gwamnan Katsina Alhaji Mannir Yakubu a matsayin mai neman takarar Kujerar Gwamnan jihar Katsina a kakar zaɓe mai zuwa. Inda yace Qs Mannir yakubu mutum ne mai ilimi, na Addini da na Boko, wanda zai iya jagoranci a duk inda ya samu kansa. Don haka cancantarsa tasa muke tare dashi da nuna goyon ba akan zamansa Gwamnan jihar Katsina domin Ayyukan ci gaba da Sabuwar ajanda.

See also  JANAR BURTAI ZAI MAKA MAHADI KOTU

Alhaji Mannir Yakubu shine mataimakin Gwamnan Katsina Aminu Masari tun daga shekarar dubu biyu da shabiyar zuwa yau, haka kuma shena Kwamishinan Noma, na jihar Katsina tun daga wancan lokacin zuwa  randa ya aje domin tsayawa takarar Gwamnan Katsina, a karkashin jam’iyyar APC

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here