JOBE YA ZAMA NA FARKO A BIYAN KUDIN FOM. na takarar gwamna.

0

JOBE YA ZAMA NA FARKO A BIYAN KUDIN FOM. na takarar gwamna.
Muazu hassan
@ katsina city news
Tsohon kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare na jahar katsina,Alhaji Farouk jobe, ya zama dan takara na farko da ya biya kudin shi don mallakar fom na takarar gwamnan katsina.
Majiya mai karfi daga hedkwatar APC ta kasa ta tabbatar mana cewa ya zuwa yau talata 26/2/2022 Wanda kudin shi na neman fom na takarar gwamnan katsina suka fara shiga asusun su shine Alhaji Farouk lawal jobe.
A jiya ne hedkwatar APC ta fitar da tsare tsaren zaben fitar da yan takarkarin ta. Da kuma bayar da asusun banki Wanda a ciki mai neman takara zai iya biyan kudin .fom da na bukatar takara.
A binciken mu Farouk lawal jobe ya zama na farko a sayen fom din takarar gwamna.
A gobe laraba ne, duk Wanda aka tabbatar da ya biya kudin shi za a bashi fom don ya cika,
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here