Wa Ya Kamata Jam’iyyar PDP Ta Tsayar Takarar Gwamna A Katsina?

0

Binciken Ra’ayin jama’a:

Wa Ya Kamata Jam’iyyar PDP Ta Tsayar Takarar Gwamna A Katsina?

@jaridar Taskar Labarai

Jaridun Taskar Labarai sun nemi jin ra’ayin ’yan jam’iyyar PDP a Jihar Katsina. Bisa tambayar a tsakanin mutane hudu da suka sayi fom a PDP, wa ya kamata jam’iyyar ta tsayar ya yi mata takara?

Wadanda suka sayi fom din sune; Sanata Yakubu Lado Dan Marke, hamshakin dan kasuwa ne. Ya yi Shugaban Karamar Hukuma. Ya yi Dan Majalisar Wakilai. Ya kuma yi Sanata. Ya nemi takarar Gwamnan Katsina har karo uku. Shi ne matashin cikin su.

Ahmada Aminu, masanin Ilmin Kimiiyar Zanen Gini ne, ma’aikaci ne da ya kai matsayin Babban Sakatare. Ya yi Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina. Ya rike Hukuma a Gwamnatin Tarayya. Yana da matsaikacin shekaru.

Shehu Inuwa Imam shi ne Dattijon cikin su. Tsohon Malamin makaranta ne. Tsohon Shugaban Kungiyar Malaman makaranta. Tsohon Shugaban Karamar Hukuma. Tsohon Shugaban Hukumar Ilmin Bai Daya ta Jihar Katsina. Tsohon Dan Majalisar Wakilai.

Na hudunsu shi ne Salisu Yusufu Majigiri, Matashin Dattijo ne. Tsohon Kansila. Tsohon Shugaban Karamar Hukuma. Tsohon Dan Majalisar Wakilai. Tsohon Shugaban ma’aikata na gidan gwamnati, wanda ya rike shugabancin jam’iyyar PDP tun da aka bar gwamnati har zuwa fitowarsa takara.

Wadannan Angunan da suke zawarcin PDP ta tsayar da daya daga cikinsu takarar Gwamna a Katsina sune muka fantsama neman jin ra’ayin jama’a a kansu.

Ya zuwa rubuta rahoton nan sune suka sayi fom, su aka tace, cikin su daya ne zai yi nasara.

Mu a jaridun Taskar Labarai cikin mutane 100 da muka ji ra’ayin su, 40 daga yankin Katsina, kuma 30 daga yankin Funtua, sai kuma 30 daga yankin Daura.

Tambaya daya ce muka rika yi wa ’yan jam’iyyar PDP. Kowane za mu kawo maka tarihin abin da muka sani game da shi. Sannan mu ba ka lokaci ka yi nazari kafin ka ba mu amsar wa ya kamata jam’iyyar PDP ta tsayar don ya yi mata takarar Gwamnan Jihar Katsina a 2023?

See also  TASHAR WUTAR LANTARKI TA BICHI DA KE KANO #GaskiyarLamarinNijeriya

Mutane 55 suka zabi Alhaji Salisu Yusufu Majigiri. Hujjarsu shi ba tsoho ba ne, ba kuma yaro ba ne. Matashin Dattijo ne. Ya dade cikin siyasa. Zai iya kare darajar ’yan siyasa. A matsayinsa na Shugaban Karamar Hukumar Mashi, da zaman sa na Dan Majalisar Wakilai. Da zaman sa na Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, ya kai ayyukan cigaba masu yawa a yankinsa.

Wannan shi ne ra’ayinsu.

Mutane 25 sun zabi Yakubu Lado Dan Marke. Sun ce matashi ne, kuma duk siyasar bai yasar da mutanen Karamar Hukumarsa ba.

Wannan shi ne ra’ayinsu.

Sai kuma mutane 15 suka zabi Ahmad Aminu ’Yar’adua. Hujjarsu zai mayar da Katsina kan ka’ida da tsari. Zai kare darajar ma’aikatan, tun da tsohon ma’aikaci ne.

Wannan shi ne ra’ayinsu.

A karshe kuma mutum biyar sun zabi Shehu Inuwa Imam. Hujjarsu Dattijo ne, kuma ya sha gwagwarmayar rayuwa, zai amfani da darasin rayuwarsa wajen kawo cigaba a Katsina.

Daga magoya bayan a kowace shiyya kuma, Majigiri kusan kowace shiyya an san shi, kuma yana da magoya baya.

Yakubu Lado magoya bayansa sun fito ne daga shiyyar Funtua da Katsina.

Ahmad Aminu kuwa, magoya bayansa daga Katsina, yayin da Shehu Inuwa Imam daga yankin Funtua yake da magoya baya.

Wannan shi ne abin da muka gano daga ’yan jam’iyyar PDP a kan wa ya kamata su tsayar a zaben Gwamnan na shekarar 2023.

Allah ya sa a yi zaben fitar da gwani lafiya.

Jaridar Taskar Labarai

@www.jaridartaskarlabarai.com

Katsina City News

@www.katsinacitynews.com

The Links News

@www.thelinksnews.com

07043777779, 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here