TAKARAR GWAMNAN KATSINA..INA KAN TATTAUNAWA..Injiniya NURA Khalil

0

TAKARAR GWAMNAN KATSINA..INA KAN TATTAUNAWA..Injiniya NURA Khalil
@ katsina city news
Injiniya Nura Khalil ya ce, ana ta tuntubar shi akan ya fito takarar gwamnan katsina a zaben 2023, yace shi kuma yanzu yana tattaunawa da iyalan shi, da makusantan shi da abokan siyasarshi.
Injiniya Nura Khalil ya bayyana haka ne, a wata tattaunawar da yayi da Babban editan jaridun katsina city news ta wayar tarho.
Injiniya yace, tun farko da ya fara siyasa ya dauke ta a matsayin wani matakala ta taimakon Al umma.
Kuma yana da kuduri da kuma tsarin da, in Allah zai bashi Matsayi da ikon Allah zai daga darajar Al umma.
Yace ya dauki siyasa wani fannin gwagwarmayar Rayuwa na Gina kasa da kuma Al umma.
Yace idan shawara ta bada yayi takara, zai fito takarar tsakanin shi da Allah.
Yace mutanen shi da yake siyasa dasu tun 1999 ana nan tare kuma an hada wata hadaka ta zumunci Wanda ba zai yanke ba har abada.
Yace yana da harkokin shi na kasuwanci,in babu Rugumniyar zabe sai ya tafi.ya habaka harkokin shi.in an dawo kuma ko zaiyi takara ko ba zaiyi ba sai ya dawo.
Injiniya yace har yanzu yana tuntuba da tattaunawa kamar yadda duk wani hukunci da Dan siyasa zai dauka sai ya dauki wannan mataimakin.
Nan da kwanaki kadan zan kammala kuma zan shelanta matsayar da na dauka .
Injiniya Nura Khalil ana kyautata zaton zai tsaya takara ne.a sabuwar jam iyyar NNPP mai alamar kayan Marmari.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here