TSAYAR DA MUSTAFA INUWA KULLE-KULLEN AMSAR MULKI A KATSINA

0

TSAYAR DA MUSTAFA INUWA KULLE-KULLEN AMSAR MULKI A KATSINA…..Wasu Sun Yi Taro A Kaduna

Aliyu Salisu
@ Katsina City News

Mun samu labari sahihi wasu jiga-jigai yan asalin Jihar Katsina sun yi taro a Kaduna, inda suka tattauna yadda za a kwace Jihar Katsina daga hannun APC.

Mun samu tabbacin a otal din da aka yi taron da kuma babban dakin da aka kama.
Mahalarta taron mafi yawan su babu ruwan su da siyasar wata jam iyya.ba wadanda aka sani bane sunyi fice a wata jam iyya. Mai mulki ko ta adawa.
Amma sun Kira kansu yan katsina masu kishi.da damuwa da halin da take a ciki.

Mahalarta taron, wasu sun zo ne daga inda suka sauka, wasu kuma a otal din da aka yi taron suka sauka.

Majiyarmu ta ce, wanda ya kira taron ya ce yanzu Katsina tana kamar kasar Rum ce lokacin mulkin Nero, dole ne a yi hada karfi da karfe waje daya a kwace ta daga jam’iyyar APC.

Mahalarta taron sun yi doguwar tattaunawar da suka zartar da tsare-tsare daban-daban.

Mafi yawan tsare-tsaren yadda za a kassara jam’iyyar APC da karfafa jam’iyyun adawa su fito da ‘yan takarkaru nagartattu.

A kan zaben Gwamna sun tsara yadda za a tabbatar da cewa Dakta Mustafa Inuwa ya yi nasara a zaben fitar da dan takara a jam’iyyar APC.

“Duk wani yarfe, ko suka ko makarkashiya a kan takarar Mustafa Inuwa ta tsaya”, yanzu a taimaka ya yi nasara APC ta fito da shi.

“Daga nan za mu fitar da duk abin da muke da shi mu yi aiki da shi, ” in ji mai ba mu labarin.
“Kayar da APC zai yi mana saukin aiki, saukin kashe kudi, da haifar guguwar bala in zabe idan Mustafa ne Dan takarar ta ” inji mahalarta taron.

See also  RIKICIN PDP YA DAUKO SABON SALO A JAHAR KATSINA

Sai dai jaridun mu ba su iya gano me mahalarta taron suka shirya in har APC ta tsayar da Mustafa Inuwa ba.

Duk tilascin da jaridun suka yi na neman jin me aka tsara, kalma biyu take fita daga bakin mutane hudu mahalarta taron da jaridun suka yi magana da su. Kalmar ita ce: “Sirri ne”.

Kawo rudu a jam’iyya ko takara a lokacin zabe ba sabon abu ba ne a siyasar Nijeriya.

A 1999 jam’iyyar PDP ta kawo rudu a jam’iyyar APP, wanda aka yi ta rikici har aka kammala zaben Shugaban Kasa.

Daga baya Olusegun Obasanjo ya ba Shugaban jam’iyyar ta APP mukamin mai ba shi shawara a kan harkokin siyasa.

A nan Katsina ma an samu haka a 2011, inda har aka samu rudun wa za a zaba tun daga Gwamna har ‘yan Majalisin Tarayya. Sai bayan zaben kotu ta rika warware turkaniyar, inda ta kwace wajen wadanda aka fara bai wa aka ba wasu.

Rudu a zaben Gwamna ya faru a wasu jihohin, wanda haka ya rika kayar da ‘yan takara.

A zaben 2023 ba mu san wane irin rudu ake son kawo wa jam’iyyar APC ba, in har ta tsayar da Mustafa Inuwa a matsayin dan takararta.

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here