KYAUTAR FAM GA CANCANTACE DAN RIMI

0

RIMI/CHARANCHI/BATAGARAWA (I stand with Rimi)

KYAUTAR FAM GA CANCANTACE DAN RIMI……

Godiya ga Ubangijin da yayi damana da sanyi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon karshe da ahalinsa baki daya.

Tun bayan dawowar mulkin damokuradiyya a shekarar 1999. Karamar hukumar Rimi ita ce farko da ta fara dana kujerar Majalissar wakilai mai wakilta kananan hukumomin Rimi da Charanchi da Batagarawa a zango na farko na shekaru hudu.

Daga wannan zangon karamar hukumar Rimi bata kara samun wannan damar ba sakamakon shirya wa da manyan Rimi suke fadin ba a yi ba, shi ya sa suke goya baya ga wasu na waje da su yi carab da kujerar har zuwa sadda za su shirya.

Wannan ya sa ni Injiniya Surajo Yazid Abukur da na kasace daya daga cikin ahalin karamar hukumar Rimi kuma wanda ya ke da ruwa da tsaki a cikin siyasar Rimi naga dacewar na yi amfani da abinda Allah ya hore man domin sawo wa Al’umma karamar hukumar Rimi fam din tsaya wa takarar kujerar Majalissar wakilai ta Rimi/Charanchi/Batagarawa na bayar da shi kyauta ga duk wani da ake ganin ya shirya kuma yana daga cikin siyasar nan, sannan yana da zumma da karsashen yin wannan takara da ya zo na bashi wannan fam din tare da alkawarin bayar da duk wata gudumuwa tare da abinda ya sauwaka na kudin yakin neman zabe da neman jama’a ba tare da wata yarjejeniya ba.

Haka kuma su mutanen da suke ganin Rimin bata shirya ba suma muna kira garesu da su je su zauna su zakulo duk wanda suke so ya zo ya karbi wannan fam din wanda aka san zai iya fitar da mutanen Rimi kunya kuma ba zai ci amanarsu ba.

Kofa bude take daga nan har zuwa awanni 24 kafin fara tantance ‘yan takara.

Sharadin dai shi ne duk wanda za a kawo a tabbatar zai iya kuma jajirtacce ne, idan ba a samu ba har lokaci ya cika to Ina neman goyan bayan duk wani mai kishin Rimi da gaske na goyan baya da fatan alheri dan zan jaraba sa’a ni na cike shi a madadin mutanen Rimi.

Na bayar da wannan damar musamman saboda kara godiya ga Allah na kara shekara da haihuwata a wannan rana 7/5/2022.

Ina wa kowa fatan alheri, Allah ya yi mana muwafaka ya kuma dubi lamurranmu ya gafarta mana kurakuranmu ya haskaka mana.

Engr. Surajo Yazid Abukur Ph.D FNSE.

Istand With Rimi….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here