NEMAN KUJERAR GWAMNAN KATSINA…WAYE FAROUK JOBE
Daga Ahmad Sani Daura
@ katsina city news
Faruk Lawal Jobe shi ne Gwamnan da Katsina, ke bukata duba da horan da ya samu a lokacin gudanar da ayyukansa na Banki, tun yana karamin ma’aikaci har kai sahun kololuwa.
Inda ya samu horo kan yadda ake gudanar da harkokin kudaden waje da kuma bincike a shekarar 1992 zuwa 1994. Tun daga nan ke halarta kwasa-kwasai, a tsakanin bankuna AfriBank da NUB da UBA da Mainstreet da kuma Skye. In da ko a shekarar 2020 ya halarci taron sanin yadda ake bunkasa harkokin jama’a.
Kwarewar ta janyo masa yin ayyukan da Bankunan, domin a rike mataimakin mai gudanarwa na Bankin Afri na Katsina. Da sauran mukamai a Maiduguri da Sokoto.
Haka ma, Banki NUB ya rike, Manajan kasuwanci a shekarar 2001 zuwa 2004 na Katsina.
A Bankin Standard Trust da UBA ya zama Manajan kasuwanci da Manajan yanki na Katsina a shekarar 2005, Sannan ya yi Manajan shiyya a jihar Kaduna da kuma Daraktan shiyya na Katsina.
Sannan ya zauna Maiduguri da Kaduna da Sokoto, inda ya rike mukamai da dama na yankunan Arewa masu Gabas, da Arewa masu yamma, har zuwa shekara 2012.
Ganin cancantarsa da rikon amanarsa ya sanya Maigirma Gwamnan, Alhaji Aminu Bello Masari, ya gayyato shi a cikin mulkinsa, ya ba shi, Mataimaki na musamman kan harkokin kuɗi a shekarar 2015 zuwa 2019.
Ganin irin gudunmawarsa kan farfaɗo da harkokin kuɗi a jahar da amanarsa, tasa a karo na biyu ya ba shi Kwamishinan kasafin kudi da bunkasa tattalin arziki a 2019 zuwa wannan shekara da ya ajiye don kansa, don neman zaman Gwamna jihar Katsina.
A wa’adin mukaman da ya rike, mai girma Gwamna ya sanya shi cikin kwamitoci da dama, kama daga yadda za a gudanar da mulki a shekarar 2015 dana yadda za a fitar da jihar Katsina daga halin matsin tattalin arziki, da bunƙasa shi da haɓaka ilmi da samar da mafita kan tsoro da bunkasa harkokin kungiyar Direbobi da kuma samar da tsarin da zai inganta harkokin Shari’a da al’umma da kuma yansiyasa.
Sannan ya yana cikin kwamitin da zai tantance ma’aikatan lafiya da inganta albashinsu da sauran hakkokin su, haka kuma yana cikin kwamitin samar da sabon tsarin albashin ma’aikata. Da kuma zama wakili na yadda za a tallafawa jawarawa a kananan hukumomi sha daya. Haka ko a shekarar da ta gabata, ya zama memba na kwamitin duba ayyukan da Gwamnatin Katsina ta aiwatar.
Duba da yadda ya gudanar da harkokin Bankuna duk da matsalolin sa, ya gama lami lafiya, har da sakayyar kambin girmamawa, da kuma yadda ya zama ja gaba wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Katsina, da katsantuwarsa cikin kwamitocin da ya shafi harkokin ayyukan gwamnati da yan siyasa da kuma inganta rayuwar al’umma, ya dace da ya zama magajin Gwamna.
Katsina na bukatar mutum masanin tattalin arziki a halin da duniya ta shiga na masassarar tattalin arziki Najeriya kuma ta shiga halin tsaka mai wuya akan kudin shiga da gudanarwa.
Wannan la akari ya kama ta deliget ya kamata su dubi Allah su su Sanya jahar a gaba.ba aljifunsu ko son ransu ba.
Muna masa fatan alheri, da addu’ar kasancewa sabon Gwamnan Jihar Katsina a shekara mai zuwa.
Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779