JAM’IYYAR PDP NA GAF DA SASANTA ‘YAN TAKARKARIN TA.

0

NEMAN GWAMNAN KATSINA:

JAM’IYYAR PDP NA GAF DA SASANTA ‘YAN TAKARKARIN TA.

Mu’azu Hassan
@ katsina city news
Jam’iyyar adawa ta PDP na gaf da sasanta ‘yan takarkarin ta guda hudu da suka fito neman kujerar Gwamnan Katsina.

Alhaji Shehu Inuwa, Ahmad Aminu ‘Yar’adua, Sanata Lado Dan Marke da Salisu Yusuf Majigiri.

Yunkurin farko shi ne na wani zama da masu ruwa daga tsaki daga jam’iyyar suka yi a Abuja.

Cikin wadanda suka halarci zaman da aka yi akwai Alhaji Lamis Dikko Ajiyan Katsina, Alhaji Labo Tarka, Tukur Mani, Lawal Rufai Safana, Sanata Ahmad Babba Kaita Shema, da kuma duk ‘yan takarkarin.

Abin da aka tattauna a taron ya za a yi zaben Gwamnan Katsina a 2023 da sauran zabubbakan? Matsalolin da ke kasa da yadda za a tunkare su.

A taron an kafa kwamitin da zai sulhunta duk ‘yan takarkarin kowane mukami har da Gwamnan Katsina.

A taron duk masu neman Gwamnan na Katsina sun bayyana korafin su, kuma an tattauna su.

Yunkuri na biyu shi ne wani zama da aka yi a gonar Alhaji Hamisu Gambo, Dan Lawan Katsina.

Zaman an yi shi ne a tsakanin Ali Haruna Jani, Dan Lawan Katsina, Yakubu Lado da kuma Salisu Majigiri.

See also  BINCIKE NA MUSAMMAN: YADDA JAM’IYYAR PDP TA FAƊI ZAƁE A JIHAR KATSINA

An ce an tattauna yadda duk wanda ya samu kujerar zai taimaki dan’uwansa a kafa gwamnati tare.

Wata majiya ta tabbatar mana cewa Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal shi ma yana nasa kokarin.

Yunkuri na baya bayan nan shi ne wanda Gwamnan Ribas, Wike yake kokarin yi.

An tabbatar wa jaridunmu cewa Gwamnan ya kira ‘yan takara biyu zuwa taro a Jihar Ribas. ‘Yan takarar sune Yusuf Majigiri da Yakubu Lado.

A waccar haduwar da za a yi ana jin za a daidaita Yakubu Lado da Majigiri, yayin da ake tsammanin Janar Ali Gusau zai shiga tsakani da Ahmad Aminu ‘Yar’adua.

An shaidi Shehu Inuwa Imam da cewa dattijo ne, wanda ba abin da yake dauka da zafi. Bukatarsa ya za a yi nasara.

Jam’iyyar PDP Ta yi lamo tana son samun arha daga matsalolin da za su iya auka wa jam’iyya mai mulki ta APC bayan fitar da ‘yan takarkarin su.

“Muna fatan a tsayar mana da ‘yan takarkarin da za su taimaka mana, ” haka wani jami’in PDP ya fada mana.

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here