YAN NEMAN TAKARA: SUN AJE AIKI SUNA ZUWA OFIS

0

YAN NEMAN TAKARA:
SUN AJE AIKI SUNA ZUWA OFIS
Suleman umar
@ katsina city news
Wani binciken da mukayi a tsakanin wadanda suka ajiye aiki don neman takara a jam iyyar APC a jahar katsina sun ajiye aiki amma suna zuwa ofis wasu ma ana zargin suna cigaba da aikin ofis din su.
Binciken mu ya gano, wasu da suka ajiye aikin suna zuwa ofisoshin su da Dare bayan an kafa ta dauke.har wasu suna gudanar da tarurrukan su na siyasa a ofisoshin nasu.
Binciken mu ya gano wasu kuma suna zuwa ofisoshin ne, lokacin hutun karshen mako da kuma lokacin hutun sallah da akayi.
Da yawan su binciken mu ya tabbatar mana basu mika ragamar tafiyar da ofis din su ga Wanda yake mafi girman mukami a ma aikatar da suke ba.
Wani abin mamaki yadda wakilanmu mu suka ga shugaban hukumar kasroma Alhaji sirajo Yazid Abukur Wanda aka nuna ya sayi fom na takarar Dan majalisar tarayya.
Amma yau talata 10/5/2022 aka ganshi ya yaje ofis din kasroma cikin motar ofis har da mai kula da lafiyar.
wakilanmu sun shaidi sai da yayi Awowi acikin ofis din.
Gaban wakilanmu, wani Dan sakon kawo takardu daga gidan gwamnatin katsina ya kawo sako aka shigar da ita.wani ma aikacin wajen yace ai har yanzu yana zuwa ofis akai akai.
Daga cikin yan takarar gwamna da suka ajiye mukaman su.Alhaji Farouk lawal jobe da Mustafa inuwa,binciken mu ya tabbatar tun da suka bar ofis din su basu kara shiga cikin harkokin ofis din ba.
Dukkanin su sun mika tafiyar da aikin ofis kamar yadda duk mai ajiye mukami aka bukaci yayi.
Haka, Alhaji Mannir Yakubu mataimakin gwamnan katsina ya fitar da kansa ga duk wata hidimar ma aikatar gona da ya ajiye a matsayin kwamishinan gona.
Ko minene matsayin doka ga Wanda ya ajiye aikin shi, ya kuma je ofis? kuma komi nine matsayin takarar Wanda ya ajiye ya kuma cigaba da zuwa ofis? Ko abokan adawa na iya kai karar Wanda ya Saba ma dokar a kotu?
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here