FAROUK JOBE: KWAREWARSA DA AYYUKAN SHI.

0

FAROUK JOBE: KWAREWARSA DA AYYUKAN SHI.

Bishir Suleiman
@ Katsina City News

Faruk Jobe Dantakara ne da zai iya bunkasa tattalin arziki Jihar Katsina. Domin kwarerar ne sha’anin harkar kudi, domin ya yi aikace aikace da dama a bangarorin hada-hadar kudade. Na bankunan Afribank da NUB da UBA da kuma Mainstream.

Ya samu gogewa kwarai da gaske a bangaren aikinsa. Don kuwa a aikin sa na Afribank, sai da ya kai babban jami’i da ke kula da hada-hadar kudade. Bayan ya rike manaja a jihohin Katsina, Maiduguri da Sokoto, daga shekarar 1997 zuwa 2001.

Duba da haka ne, ya amsa gayyatar NUB International Bank LTD, inda ya yi aiki a matsayin Manajan Kasuwanci tun daga shekarar 2001 har zuwa 2004.

Jajircewarsa da samar da cigaba a harkokin Kasuwanci, ya sanya Bankuna neman yin aiki da shi, don bunkasa huldodinsa.

Don haka ne, Bankin Standard Trust Bank/ United Bank For Afrika suka ba shi, matsayin Manajan Kasuwanci a Katsina a shekarar 2004 -2005 sai matsayin Area Manaja a shekarar 2005 – 2006 a Katsina, sai kuma Regional Manaja a shekarar 2007 – 2008 a Jihar Kaduna, ya sake dawowo Katsina ya zama Babban Darakta na Shiyya a Katsina, a shekarar 2008 – 2012.

Saboda kokarinsa da jajircewarsa, ta ba shi halarta kwasa kwasai da dama a tsakanin Bankuna da ya yi aiki da su. Domin ya halarci, horaswa a shekarar 1992 – 1994 kan sannan harkokin kudi da mu’amula da su na gida dana waje da kuma bincike.

A shekarar 1999 ya samu halarta horo na sanin hanyoyin bunkasa adana kudade, da kuma kwas kan yadda ake sarrafa na’ura mai kwakwalwa.

Sannan a 2003 ya halarci horo kan matsalolin harkar kudi da tsarin tafiyar da su. A IBFC Augusto Training LTD.

Sannan yana da horo da ya samu a 2007 kan kwararan matsanin harkokin kudi. A leadership & Vision Limited. Haka a 2008 ya hora kan sanin fitattun halaye guda bakwai na cikakken Mutum. Duk dai a shekarar ya samu hora kan sanin hanyoyin samun nasara ga Daraktan Shiyya. A UBA Academy

Amana mai kara kwarjin mutum, don da rikon amanar sa ne, ya kai shi ga haka, har ya halarci horo kan tsarin haddaka, a shekarar 2013 Haka ma, a 2014, ya samu hora kan yadda kyakkyawan shugabanci kan haifar da aiki tukuru da kuma zaman lafiya a tsakanin kabilu. Ko a shekarar 2020 ya samu horo kan yadda za a shayo kan matsalolin wata annoba da ta janyo durkushewar da harkokin al’umma.

Yana daga Fitattun ayyukansa a Bankin UBA, ya samar da mafita a yankuna Arewa Maso Gabas, mai mazauni Maiduguri, a shekarar 2009 da Arewa Maso yamma, mai mazauni a Kaduna, da kuma Sokoto a shekarar 2010 – 2012.

Ko a Bankin Mainstream ya rike Manajan Shiyya na Katsina da Sokoto amdaga shekarar 2012 zuwa 2015, har ta kai shi ga rike, Maitamakin Babban Manaja.

Wadannan ayyuka nasa a Banki ya samar masa da kanbin girmamawa da dama, daga cikin su har da Wanda aka ba shi a shekarar 2003 Kan Ma’aikaci na Musamman ( CEO’s Best Staff Award) daga NUB Intl. Bank LTD. Da kuma wakili na Musamman ( CEO’s Award – Best Brank Ambassador) a shekarar 2007 daga UBA PLC

Da Jin wadannan ayyukan za a fahimci Katsina na bukatar Faruk Lawal Jobe a matsayin Gwamnan Katsina, don da kokarinsa ne, Gwamanatin Aminu Bello Masari ta janyo don bayar da gudunmuwarsa.

A biyo a ji rawar da ya taka.
katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here