HARKAR DABANCI A KATSINA: Wani Matashi ya Kashe ɗan gudun Hijira..
Zaharaddeen Ishaq Abubakar @ Katsina City News
Ana Zargin Wani Matashi a ƙaramar Hukumar Batsari da kashe wani yaro mai kimanin shekaru goma sha uku, a garin Batsari, yaron gudun hijira ne da suka fito daga garin waziri, sakamakon harin ‘yan Bindiga da suka addabi yankin inda suka samu mafaka shi da iyayensa a garin Batsari, kimanin watanni uku, baya har takai yaron da ake zargin ya mutu ta dalilin Duka l. Yaron mai suna Umar ya dan fara sana’ar saida Mangoro domin taimakawa iyayen sa.
Amma daga bisani a ranar Lahadi, wani Ɗandaba mai suna Muhammadu ya je har wajen da yaron ke sana’arsa, ya sha Mangoro kuma yayi ta bugun sa, wanda yayi Sanadiyar mutuwar sa a Ranar Talata.
Wakilin Katsina City News ya zanta da mahaifin yaron inda ya tabbatar da Dansa lafiyar sa kalau amma tunda ɗan daban ya bigeshi ya dawo gida bashi da lafiya kwana biyu yace ga garinku nan, inda yace; “amma yaron da yayi bugun ya gudu.”
Jami’an tsaro na garin Batsari sun kama mahaifin yaron mai suna Ummaru Galadima daga bisani kuma suka sake shi. Izuwa hada wannan rahoto har yanzu babu wani mataki da iyayen yaron suka iya dauka koda na Shari’a kasantuwar ta kansu suke basu da karfi kamar yanda mahaifinsa yaron ya tabbatar wa wakilin namu.
A watanni biyu da suka gabata Gwamnatin Katsina ta kafa wani kwamiti da zai yi yaƙi da harkar Dabanci, Shaye-shaye da Bangar Siyasa, a karkashin mai bawa Gwamnan Katsina shawara a kan harkar tsaro, wanda ko a shekaranjiya Kwamitin ya samu nasarar daƙile wasu matasa masu harkar.
A wani bincike da Jaridun Katsina City News suka gudanar na jin ra’ayin al’uma da masu ruwa da tsaki akan hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da masu kula da Asibitin masu lalurar taɓin hankali, sun tabbatar mana da cewa kashi tamanin da biyar na mahaukata suna samuwa ne daga shan miyagun kwayoyi.
Katsina City News
The Links:
Taskar Labarai: