MATASHI MASANIN KIMMIYYAR ILMIN YANAR GIZO YA FITO TAKARA A KAITA/JIBIA ..ISIYA ADO KAITA.
Bashir Suleman
@ katsina city news
Wani masanin ilmin kimmiyyar yanar gizo, Wanda samu horon sa a kasar ingila da turai ya fito neman takarar Dan majalisar tarayya karkashin jam iyyar PDP a kananan hukumomin kaita da jibia.
Masanin Wanda a irin karatun da yayi da kuma manyan makarantun da suka horas dashi a kasar ingila da wuraren da yayi aiki a kasar ingila. Duk katsina babu matashi mai kwali da kwarewa irin tasa a fannin da yake , Ya fito nema takara don kishin jahar katsina da kuma yankin da ya fito.
Isiya Ado kaita ya fada ma jaridun katsina city news cewa na fito ne, don a neman wannan takarar don kishin jaha ta da kananan hukumomin mu da kuma kasa ta.
Yace, wannan bashi bane karon farko Dana fito, na fito takara a a zaben 2019,Allah bai bani ba, na fadi tun a zaben fitar da gwani.Ban damu ba.yanzu ma na kara fitowa takara don kishin al umma ta.
Masanin yace, duk ilmi na akan kimiyya na karanta a manyan makarantun ingila tare da manyan masana a duniya da suke aiki a kamfanoni masu kawo kudi, amma ba kudin ya ke gaba na ba, Al umma ta.jaha ta da kasa ta.
Alhaji isiya Ado yace,yace na fito gidan siyasar PDP ne, inda naga yadda ake taimako da hidima da jama a, wannan ya Sanya na gane ta siyasa ce kawai zaka shiga jama a a sanka ka kuma gwada kishin su akansu.
Isiya Ado yace ina da tsare tsare da idan Allah muka kai ga gaci sai yankin da na fito ya zama abin misali a jahar katsina da Najeriya baki daya.
Da muka Nemi jin ra ayin mutane a karamar hukumar kaita da jibia da yawa sun nuna goyon bayansu a gare shi.
Inda suka ce, wakilcin majalisar tarayya dama kamata yayi ya zama Wanda.idanshi da karatun shi ya bude Wanda babu abin da zai bashi tsoro.
Don haka ya kamata a rika jaraba irin wadannan masana kuma matas.