Hanyar Nasara na Tare Cancanta: Jibia/Kaita ga Isiya Ado 2023
Bishir Suleiman
@ Katsina City News
Masani ne a harkokin kasuwanci da kuma fasahar Na’ura mai ƙwaƙwalwa, kuma goge ne domin ya yi aikace aikace da dama a cikin gida da kuma kasashen waje.
Domin kuwa ya yi aiki da Babban kamfanin nan na duniya dake London wanda ya gwamance kan sayar da kaddarori, musamman na Gidaje don yana daya daga cikin wadanda suka kara bunkasa kamfanin ta hanyar samar masa da cinikin sama da Dala Biliyan biyu a shekarar 2008
A cikin gida Nijeriya ma ya yi aiki da hukumar Gidaje ta Kasa, inda ya rike matsayin Mataimakin Manaja na kimiyar hanyoyin sadarwa na zamani na hukumar a shekarar 2009 zuwa 2018.
Na daga cikin ayyukansa a hukumar tsara yadda za a samar da filaye da tabbatar da rigistar (CLPR) wanda hakan ya samar wa gwamnatin da kudin shiga sama da Biliyan Biyu da kuma gano filayen da aka rasa sama da guda 1500. Sannan ya kawo tsari na zamantar da ayyukan hukumar, kuma kokarin sa ne ya haifar da samar da gidaje a daukacin fadin kasar nan, ta hanyar tattara zunzurutun kudade sama da Dala Biliyan Ashirin da biyar a shekarar 2019.
A bangare guda kuma ya san halin da yankin da yake neman wakilta ya ke ciki, domin kuwa ya ayyana cewa a cikin wa’adin dawowar siyasa kama daga shekarar 1999 zuwa yau sau daya, Mahaifarsa ta taɓa tura wakili a Majilisar wakilai ta kasa. Karamar Hukumar Jibia ce ta kwashe shekaru a ashirin tana wakiltar Jibia/ Kaita.
Don haka akwai buƙatar kara yunkurin ciyar da yankunan nasu gaba, ta hanyar bunkasa tattalin arzikin yankin da kuma samar da ababaden more rayuwa wanda zai farfaɗo da mutanan yankin.
Muddin aka bai wa Isiya Ado daga karamar hukumar Kaita damar wakiltar yankin Jibia/Kaita a kakar zabe mai zuwa na 2023, za a ga kyakkyawan wakilci mai cike da san Barka, domin mutun ne mai gogewa da sanin makamar aiki da aiki tukuru.
Na daga cikin kudororinsa guda hudu indan Allah ya kai shi majalisar wakilai ta kasa, a yankin nasa.
1) Bunƙasa hanyoyin tattalin arziki da yakar talauci.
Ya yi tunani mai zurfi kan yadda za samar da ayyukan yi a yankin nasa da bunkasa hulɗar hada hadar kasuwanci tsakanin iyakokin mazabarsa ta Jibia/Kaita da kasashe Makwafta, da lamunin kasuwanci tsakanin Bankunan da al’ummar mazabarsa.
2) Bunƙasa Ilmi: Na daga cikin kudororinsa samar da hanyoyin da al’ummar mazabar sa ta jibia/Kaita, ta yadda zai samar da tallafin karatu da kuma ilmantar da al’ummar sa ilmin sana’o’i, dangogin kafinta, Na’ura mai ƙwaƙwalwa, hoto, zane, kanikanci, gyaran ruwa, fanti, walda, harkokin noma da hulɗar hatsi da gyare-gyaren na kayayyakin wutar lantarki da sauransu.
3) Kula da harkokin lafiya: Ganin cewa lafiya babbar jari ce ta sanya zai mayar da hankali wajen tallafawa lafiyar iyali don rage mace macen mata masu juna biyu, zai samar da kayayyakin gwaje da kuma saukaka masu wahalhalun da sukan fuskanta ta hanyar samar da haɗaka da hukumar insorar lafiya ta kasa.
4) Tallafawa bangaren sufuri: Ya ga cewar mazabunsa na da kusanci da iyakar jumhuriyar Nijar, don haka sufuri na daga cikin abin da ake bukata da kuma samar da kudaden shiga ga al’ummar yankin, tasa zai samar da ababen hawa ga mutanen yankin ta hanyar hadin guiwa da hukumomin bayar da lamuni, don samar da abin yi da kuma saukakawa al’umma ta bangaren sufuri.
Wadannan kudurori na Isiya Ado da su ne, zai farfaɗo da tattalin arzikin yankin nasa wanda kuma yankin nasa zai tserewa sa’o’insa dake a fadin ƙasar nan.
Duba da haka ne Ado Isiya Kaita ya zama mafi cancanta wa al’ummar Jibia/ Kaita, domin masanin ne da ya haɗa fannoni da dama, sannan kuma yana da wayewa da gogewa ta ayyuka ciki da wajen kasar nan.
Babu shakka al’ummar mazabar Jibia/Kaita za su dara a zaben Isiya Ado a matsayin dan Majilisar wakilai ta kasa, a kakar zaben 2023
Bashir Suleman Marubuci ne a jaridun katsina city news.
@ www.katsinacitynews.com