JOBE; RAYUWARSA DA HARKOKIN KASUWANCI SHI.

0

JOBE; RAYUWARSA DA HARKOKIN KASUWANCI SHI.
Bishir Suleiman
@ katsina city news
Duk rayuwar aikin shi a bankuna daban daban yayi.kuma an rika canza masa wajen aiki daga nan zuwa can.
A shekarar 2000 ya maido iyalan shi katsina kuma inda suke zaune tare da al umma har yanzu.
Ya fara zama a unguwar layout daga baya ya koma garin dandagoro tsakiyar jama a yana tare da mutane kullum.”ya “yan sa da iyalan shi, na hudda da sauran jama a.
Yana da karfin ikon mayar da iyalan shi Kaduna ko Abuja ko da kuwa legas yake bukata.amma ya gwammace ya zauna katsina da iyalanshi.
Jobe hamshakin manomi ne,tun shekarar 2007 yake da wata katafaiyar gidan gona Wanda suke noma da kiwo kala kala.da ma aikata daban.
Yana noma wurare daban Daban a jahar katsina.wadanda ya samar wa aiki a gonakin shi suna da yawa gaske.
Yana da makaranta mai suna IJaba academy a garin dandagoro makarantar na cikin wadanda suke da tsari da ingancin koyarwar a jihar katsina.ginan na ce da aka Gina a tsarin ilmi da koyarwa.
Yana da jari a kamfanoni daban daban .yana kuma harkar sayen gidaje ya gyara ya sayar a Kaduna da Abuja .
A shekarar 2015 da suka shigo gwamnati duk abokan tafiyar siyasar,sun San jobe yana da rufin asiri.
A zaman sa na Dandagoro ya kai masu aikin hanyar ruwa wadda ke matsa masu.ya yi niyyar bada kashi mafi tsoka al umma suyi aikin .
Amma daga baya ya sanya gwamnati tayi aikin.
Jobe dan kasuwa ne, da harkokin kasuwancinsa suka samar wa dimbin mutane aiki.A gonakin shi,makarantar sa, da harkar sa ta sayen gidaje a gyara ya sayar.wasu kuma sun samu aiki ta kamfanonin da yake da hannun jari a cikin su.
JOBE BA CIMA ZAUNE BANE, DAN JIRAN A BASHI KO TA FADI KASA GASASSA.
katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here