Dattako Shi ne Amana: jihar Katsina 2023 sai Mannir Yakubu.

0

Dattako Shi ne Amana: jihar Katsina 2023 sai Mannir Yakubu.

Hali abokin Tafiya, dattako da hangen nisa shi ne, cancanta, don haka ne ma Hausawa kan ce magana Daya sai dattijo. Alhaji Mannir Yakubu, ya tabbata cikakken dajito Mai dattako, wanda ya dade a cikin siyasar adawa, domin ganin an kyautata ratuwar al’umma.

Shi ne jajirtaccen dansiyasa masani a kan kididigar gine – gine, wanda bai taba sauya jam’iyya ba, balle ya yi hannun riga a tafiyar Amana ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi takarkaru da dama, a jam’iyyar ANPP har ya zuwa lokacin assasa jam’iyyar CPC inda ya yi takara Gwamnan jihar Katsina, har kawo lokacin da aka samar da jam’iyyar APC yana daga cikin kanwa uwar gami na kafuwarta.

Ganin dattakonsa da gogewar sa, da jajircewa kan tafiyar adawa ta sanya Mai girma Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya jayo shi a matsayin wanda zai tamaka masa tafiyar da gwamnatin Katsina, a shekarar 2015, ganin gaskiya da rikon amanar sa da yadda ya ke tallafawa gwamnati maigidansa ta sanya aka kara zabensu a 2019, wanda har kawo yanzu ya ke a matsayin Matamakin Gwamnan jihar Katsina.

See also  TSOHON KAKAKIN MAJALISAR KATSINA YACI KUDIN ZABE

Kokarinsa a kan tafiyar da kwamishinan ma’aikatar gona, ta Jihar kataina, ya kara fito da aikace- aikacen sa da ya yi tun katsina bata samu jiha ba, muna hade da Jihar Kaduna, wajen bunkasa ma’aikatar ayyuka da gidaje da yadda aka tsara jihar Kaduna da sauye sauye masu inganci da ya kawo.

Alhaji Mannir Yakubu, cikakken mai kishin Jihar Katsina, kuma Mai gaskiya da rikon amana, wanda duk mai kishin Jihar Katsina, zai so ya zama magajin Gwamnan Masari, ganin yadda bai mai jin kansu a tsawon lokaci, haka kuna mutum ne, wanda ya damu da halin da jihar Katsina ke ciki.

Al’ummar Katsina za ta yi alfahari kwarai da shi a kasantuwar sa Gwamnan a zabe mai zuwa. Duba cancanta da shi ne kishi, cancanta na tare da dattako da gaskiya da rikon amana da gogewa kan tafiyar da mulki da kuma sanin halin da jihar take ciki, dukkan wadannan halaye ne na Mannir Yakubu, Katsinawa Dattako shi ne Amana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here