AN KAI MUMMUNAN HARI A WANI GARI A BATSARI

0

AN KAI MUMMUNAN HARI A WANI GARI A BATSARI
…….An kai wani harin a kasuwa.

Misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news

A daren jiya lahadi 29-05-2022 da misalin 10:30pm wasu mahara ɗauke da muggan makamai suka kai hari ƙauyen Zamfarawa mai nisan kilomita biyu daga gabaccin Batsari dake jihar Katsina.
Maharan sun tafi dabbobin garin masu tarin yawa. Mutane ƙauyukan dake yankin suka bisu da nufin sai sun ƙwato dabbobin. Yunƙurin ya haifar da masayar wuta tsakanin su wanda yayi sanadiyyar kashe mutane bakwai (7) cikin daga ɓangaren masu yunƙurin ƙwato dukiyar, amma sun samu nasarar ƙwato dabbobin, saidai abinda baa rasa ba suka iya tafiya da shi. Bamu samu tabbacin kashe ko ɗaya daga ɓangaren ƴan bindiga ba.

See also  HARE-HAREN 'YAN BINDIGA NA KARA TA'AZZARA A YANKIN BATSARI.

Harin ƴan bindiga ya zame ma mutanen yankunan karkarar ƙaramar hukumar Batsari ruwan dare, domin ko a kasuwar Ƴandaka dake ci jiya lahadi sa da mahara suka kai hari ana cikin cin kasuwa inda suka harbi wani mutum ga cinya sannan suka kwashi dukiya da ƴan kasuwa suka gudu suka bari.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
070437777245.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here