Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yuni, jam’iyya mai mulki ta cire wasu mutane 10 masu san tsayawa takarar shugabancin kasa.
DAILY POST ta ruwaito cewa Shugaban Kwamitin tantance Shugaban kasa kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun ne ya bayyana haka a yau Juma’a a Abuja lokacin da ya mika rahoton kwamitin ga jam’iyyar.
Har yanzu dai ba a bayyana masu neman takarar da aka soke ba.