RIKICIN ZABEN MUSAWA: ABIN DA SANI ..Alhaji Mamuda Lawal Musawa ( Mai zamani)

0

RIKICIN ZABEN MUSAWA:
ABIN DA SANI ..Alhaji Mamuda Lawal Musawa ( Mai zamani)
@ katsina city news

Sunana Mamuda Lawal Musawa, Dantakarar majalissar dokoki ta tarayya, a mazabar Musawa Matazu. Wannan ba shi bane takarata ta farko ba, karkashin wannan jam’iyya kuma a wannan kujera. Na yi a shekarar 2019 kuma cikin ikon Allah, abin da ya faru ya faru, na ci gaba da hidimomina har Allah ya kawo mu wannan lokaci.

Mun sayi fom, mun yi duk abin da ya kamata, domin tsayawa takara, kuma har ranar da aka shirya za a zabe, mun je karamar hukumar Musawa, na bar Katsina, na isa Musawa wajen karfe 7:30 zuwa 8:00, bayan na isa gidana na zauna cikin mutane na, muka ci abincin safe , Muna zaune muna wasa da dariya muna tsamanin wajen karfe 10:00 za a fara wannan zaben fitar da Dan takara , muka jira har wajen karfe 4:00 na yamma, babu wani bayani, saboda haka sai wani daga cikin yantakarar, sai ya kira ni, ya ce “Ina Musawa”? Na ce ehh ” ya ce gashi nan zuwa shi ma”, na ce to,sunan shi Alhaji Ali Maikano.

Shi ma D. Murtala wasu suka fada masa muna a gidana na, shi ma ya kira ni, na ce mai ya zo don ina gida Musawa.

Muka zauna muka yi shawara, muka ga ba za ta yiwu mu yi ta zama nan ba, saboda muna matsammanin daliget din mu da muka yi shirin za su zabe mu, su na party office, to mu tafi can mu same su, sai muka fara zuwa wa filin zabe, muka ga babu kowa, sai jami’an Yansanda na gadin wajen, muka shiga muka ga babu kowa, sai mu ka tafi party office, can ma muka ga babu daliget din nan.

To, a haka sai muka fahimci akwai matsala, sai muka kira taron menama labarai , mun yi hira daya a wurin zabe, sai muka yi wata hirar a secretariat ta party, muna tsaye nan, muna magana sai muka ji hayya- hayya.

sai kuma muka ji kayya-kayya, yandaba da yantauri muke zargin an dauko su daga wasu garuruwa, don an ce mana an ga motoci a gefen gari.

So, an gaya mana daliget dinmu suna gidan Abubakar Musawa shi ne, Matamakin Shugaban Jam’iyyar na jiha baki Daya, kuma muna da audio da hotuna da videos, inda ya tara su a gidan shi ya kulle, daliget din nan, musamman Mata, ya ce “mata suna da nakasu, za a yi saurin rinjayar su, saboda haka ya kulle su a cikin daki, nan suka yi fitsari nan suka yi sallah a ciki.

So, a wannan hali aka sanar damu ya kulle su, kuma gashi nan ma, za a kwace masu waya, don kar ma su kira wani, to a wannan muna da shaidu kamar yadda na gaya maka.

To, wannan al’amari dai ya faru gaskiya, bisa ga rashin adalci da aka yi. Su kuma daliget din nan an boye su.

Dana ga tashin hankali ya yi yawa, sai mutane suka ce mana mu bar garin nan, kar abin ya tsananta a kashe rayuka, so sai muka bar gari. Ina cikin Charanci za mu yi sallah, sai muka ji sanar an ma gama zabe, Dantakarar Bala Abu musawa Abdullahi Aliyu ya cinye kuri’u baki daya.

To, jin wannan muka san wasan yara ne, kuma tsari ma na doka na Jam’iyya ya hana ka kwashi daliget ka kai gidanka. Nan sai muka ji wai har an kashe mutane, kuma aka yi ta yada hotuna.

.To, a takaice, wannan shi ne abin da ya faru, inda an mana zabe, aka ce bamu ci ko kuri’a daya ba, to, mun san Allah ke bada wa, sai mu dangana mu hakura. To, amma a yadda ake ciki zamu dauki duka doka da Oda, domin mu nemo hakkin mutane, yancin mutane da namu hakkin, shi yasa muka hadu mu uku mu ka yi takarda muka aika da ita ga Jam’iyya da mai girma Gwamna, domin a bi mana hakkinmu a soke wannan a yi zabe, in aka yi zabe, bamu ci ba sai mu hakura, a takaice wannan shi ne bayanin dana rubuta.

Katsina City News: To, takardar da ake cewa kun rubuta, a mamadin kai ka rubuta ko ku duka ukun?

Mamuda:A’a kowa ya rubuta takarda saboda dukkanmu kowa Dantakara ne, mun dai fahimci dai akwai rashin gaskiya da aka yi mana mu duka. Shi yasa muka hadu tare muka je mu tabbatar da haka.

To, mun gama wannan kuma ka ga dole kowa ya je ya nemi Mafita, kowa ya rubuta takarda shi da sunan shi ya kai wa Gwamna, tare da uwar Jam’iyya, kuma kowa ya yi bayanin abin da ya sani tsakanin shi da Allah, da tunanin za a canza, saboda Allah ba ai zabe ba a Musawa.

Ga bayin Allah da aka kashe, ina mamakin wannan abu Musulmi ya shiga turbar da zai zo a dauki ran mutum. Alllah ya sawaka.

Katsina City News: Su wa aka fi zargin ya karkata, saboda bincikenmu ya tabbatar da yandabar nan ba yanmatazu ko Musawa ba ne kamar dauko su aka yi daga waje suwa aka fi zargin su suka dauko su?

MAMUDA: ku yan danjarida ne, zan baka misali sai kai ma kanka hisabi, ka kaddara wanda ake zargin ya dauko yandabar nan ya dauko su, to, za su kashe kansu ne da kansu? Ai basu kashe kansu da kansu sai an samu, wasu. To, kuma wadannan su ma sai ka duba ka gani, so aka yi a samu dama a tsorata mu a firgita mu, domin a yi abin da ake so. To, mun ji bayanai akwai tsohon Danmajalisa shi ya kwaso yandaba, mun ji wadannan bayanai amma bamu da tabbacin haka, amma da suka zo din, sun tarar da wasu ne, ko kuma in ka lura mu aka yi wa ba daidai ba, saboda mu dama ake son a yi ma ba daidan ba, aka kwaso yandaba, saboda al’amarin duk mai hankali yasan inda laifin nan yake, muna da hujjoji na hotuna da audio da videos na duk abubuwan da suka faru, kuma muna samun damar da za mu bayyana su, za mu fadi, kuma zamu gwadawa mutane sun yadda abin nan yake, wannan abu ne zahiri kowa yasan wadanda suka yi wannan ta’addancin kowa yasan wadanda suka yi wannan kisan kai, sai dai a ki tsayawa a yi abin da ya kamata, wannan shi ne

Daga
Muazu hassan
Bashir Suleman da
Suleman Umar
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here