Hukumar NAHCON ta bayyana kudin aikin Hajji, Yan Najeriya za su biya N2.5m

0

Jaridar daily Nigeria ta ruwaito Hukumar jindadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta sanar da biyan kudin Hajjin bana na shekarar 2022, inda ta ce maniyyatan Najeriya daga Kudancin Najeriya za su biya N2,496,815.29, yayin da takwarorinsu na Arewacin kasar za su biya N2,449,607.89.

Wata sanarwa da kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce jihohin Adamawa da Borno za su biya Naira 2, 408, 197.89 saboda kusanci da kasar Saudiyya.

Ta ce kudin tikitin jirgi shi ne babban banbancin kudin aikin Hajji.

“Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya sanar da hakan a yau, 4 ga watan Yuni, 2022 a wata ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai musulmi a hedikwatar hukumar Hajji ta NAHCON.

“Bayan sanarwar kudin, daukacin shugabannin hukumar jin dadin Alhazai ta Jiha da sauran mahalarta taron sun baiwa hukumar NAHCON farin jini bisa yadda suka yi kyakkyawan aiki wajen ganin an rage kudin aikin Hajjin kasa da Naira miliyan 2.5 duk da kalubalen da ake fuskanta.

Taron ya yaba da kokarin da Shugaban Hukumar NAHCON ya yi na samun wannan nasara a madadin Alhazan Najeriya,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here